A Karshe, Kotu Ta ba da Belin Matasa da Ke Tsare kan Sanya Rigar ‘Tinubu Must Go’
- Wata kotun majistare a Maiduguri ta bayar da belin mutane biyar da aka kama bisa zargin adawa da Bola Tinubu
- ’Yan sanda sun ce sun kama mutanen da wasu kayayyakin da ake zargin tabar wiwi, ƙwayoyin D5 da tukunyar shisha
- Lauyan masu shari’ar ya tabbatar da sakin mutanen, tare da kira ga matasa su kiyaye doka yayin amfani neman ’yancinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Wata kotun majistare da ke Maiduguri, Jihar Borno, ta bayar da belin mutane biyar da aka kama kan yin adawa da Bola Tinubu.
An tsare matasan ne bisa zargin sanya rigar siyasa mai ɗauke da rubutun 'Tinubu Must Go' a jihar Borno.

Source: Original
An kama waɗanda ake zargin ne a ranar 25 ga Satumba a Maiduguri, lamarin da ya haifar da muhawara kan ’yancin faɗar albarkacin baki da haƙurin siyasa a jihar, cewar Daily Trust.
Abin da yan sanda ke zargin matasan
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta ce mutanen ba wai rigar siyasa kaɗai aka same su da su ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.
A cewar ’yan sandan, jami’ai sun kwato kunshin tabar wiwi da ake zargi guda 15, allunan D5 guda 100, tukunyar shisha da almakashi.
Sun kuma ce an kwato riguna guda biyu da ke ɗauke da rubutun da ake takaddama a kai, yayin da wasu suka zargi jami’an tsaro da kai wa masu zanga-zangar lumana hari.
Sai dai rundunar ’yan sandan ta musanta zargin, inda ta ce ba ta goyon bayan wata jam’iyya ko ɓangaren siyasa, kuma tana bin doka yadda ya kamata.
Rundunar ta ce ta miƙa batun zuwa kotu ne domin tabbatar da bin tsarin shari’a da kuma ba kowane ɓangare damar kare kansa.
Lamarin ya ƙara ɗaukar zafi ne bayan wasu zarge-zargen da suka danganta Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, da kamen mutanen.

Source: Facebook
Lauya ya tabbatar da sakin matasan
A zaman shari’ar, lauya Alkali Askira, shugaban reshen Garki na Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya, NBA, ya tabbatar da cewa an saki mutanen bisa beli.
Lauyan ya jaddada muhimmancin ’yancin faɗar albarkacin baki, amma ya shawarci matasa da su kasance masu bin doka da oda.
Ya kuma gargadi matasan da su guji ayyukan da za su iya jefa su cikin matsala ko sa su karya doka ba tare da sani ba.
Iyalan waɗanda ake zargin sun nuna godiyarsu ga tawagar lauyoyin da suka tsaya tare da ’ya’yansu yayin shari’ar, cewar Punch.
Sun kuma ƙarfafa wa matasan jihar gwiwa da su kasance masu bin doka tare da kauce wa duk wani abu da zai iya jefa su cikin matsala.
'TinubuMustGo: Zulum ya musanta umartan kama matasa
An ji cewa Gwamna Zulum ya yi watsi da sanarwar ADC kan zargin cewa ya yi barazanar kama masu sanya riga mai rubutun “Tinubu Must Go”.
Kakakin gwamnan ya ce ADC ta dogara ne da rahoton da bai dace da ƙa’idojin aikin jarida ba wajen yin zargin.
Gwamnatin Borno ta ce jawabin Zulum ya shafi tsaro da yaƙi da miyagun laifuffuka ne, ba jam’iyyar ADC ko wata ƙungiyar adawa ba.
Asali: Legit.ng


