Ana Shirin Zaben 2027, Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Koma Baya

Ana Shirin Zaben 2027, Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Koma Baya

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin mambobinta sun sauya sheka
  • Masu sauya shekar sun ce sun yanke shawarar bin Sanata Mustapha ne saboda biyayyarsu gare shi da kuma irin jagorancin da yake yi
  • Shugaban masu sauya shekar ya ce za su haɗa kai da sauran mambobin PDP domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - Ƙarin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a mazabar Alanamu, ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma ta jihar Kwara, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

An ce masu sauya shekar, waɗanda suka fito daga rumfunan zaɓe daban-daban a ƙaramar hukumar, magoya bayan Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha, ne.

Mambobin APC sun koma PDP a Kwara
Shugaban jam'iyyar APC na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce an karɓe su a hukumance cikin PDP ne ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2026 yayin wani gangamin jam’iyyar da aka gudanar a sakatariyar PDP ta mazabar Alanamu.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Shugabannin jam’iyyar mai adawa da sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron karbar masu sauya shekar.

Sauya shekar ta biyo bayan ficewar Sanata Mustapha

Sauya shekar ta faru ne makonni kaɗan bayan Sanata Saliu Mustapha ya fice daga APC ya koma PDP a watan Agustan shekarar 2026.

Sanatan ya bar APC ne bayan doguwar rashin jituwa da ta faru a cikin jam’iyyar mai mulki.

Saliu Mustapha ya taɓa neman tikitin APC na takarar gwamnan Kwara, amma Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Yakubu Danladi-Salihu, ne ya lashe zaɓen fitar da gwani.

Daga baya Sanata Mustapha ya samu tikitin PDP na takarar kujerar Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya a zaɓen 2027.

Masu sauya sheka sun ce sun bi Saliu Mustapha

Da yake magana a madadin sababbin mambobin PDP, shugaban masu sauya shekar, AbdulRazaq Adio, ya ce biyayyarsu ga Sanata Saliu Mustapha ce ta fi rinjayar shawarar da suka yanke.

Adio ya ce za su ci gaba da kasancewa tare da sanatan ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya zaɓi yin takara a ƙarƙashinta ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun yi masa raddi mai zafi

"Muna nan ne saboda shugabanmu, Sanata Saliu Mustapha. Fitaccen ɗan siyasa ne da kowa ke ƙauna. Za mu ci gaba da mara masa baya duk inda ya zaɓi ci gaba da harkar siyasarsa.” In ji shi.

Sun yaba wa Saraki da jagorancin PDP

Adio ya ƙara da cewa shugabancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, da kuma abin da ya bayyana a matsayin sabon salon jagorancin PDP a jihar Kwara, sun ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Ya ce sababbin mambobin na PDP a shirye suke su yi aiki tare da sauran magoya bayan jam’iyyar domin samun nasara a zaɓen 2027.

“Mun kuma samu ƙwarin gwiwa daga jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, da kuma alkiblar PDP a jihar Kwara."
“Muna da yakinin jagorancin jam’iyyar kuma a shirye muke mu yi aiki tare da sauran mambobi domin samun nasara a 2027,” in ji shi.

PDP ta ce sauya shekar za ta ƙarfafa jam’iyyar

Adio ya kuma gode wa shugabannin PDP na mazabar Alanamu bisa karɓar sababbin mambobin.

Ya ce zuwansu PDP zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi wajen tattara magoya baya da kuma faɗaɗa ayyukan siyasa a matakin ƙasa, musamman yayin da ake shirin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kasa za ta yi saiti, Tinubu ya juyo kan abin da ya fi damun yan Najeriya

APC ta rasa wasu mambobinta a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kusa a APC ta koma NDC a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar tare da magoya bayanta zuwa jam’iyyar NDC.

Ta bayyana cewa magoya bayanta daga ƙananan hukumomi 14 na jihar sun bi ta zuwa sabuwar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng