'Ko Makiyana Sun San Ni ke da Kano,' Kwankwaso Ya Yi Martani ga Ali Modu Sheriff

'Ko Makiyana Sun San Ni ke da Kano,' Kwankwaso Ya Yi Martani ga Ali Modu Sheriff

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, ya yi shifcin gizo a lokacin da ya ce Peter Obi ba zai samu kuri'ar Arewa ba
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC ya yi zargin Ali Modu Sheriff ya yi kalaman ne domin ya faranta wa masu mulki a fadar shugaban kasa
  • Kwankwaso ya kuma ce Obi ya taba nuna karfinsa a Arewa bayan ya samu sama da kuri'u miliyan biyu a yankin a zaben shugaban kasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da ikirarin tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff.

Ya ce babu kamshin gaskiya a cikin kalaman Ali Modu na cewa 'yan Arewacin Najeriya ba za su zabi Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Kwankwaso ya yi raddi ga Ali Modu
Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Idon Mikiya/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Channels Television, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Sheriff ya yi kwanan nan game da dan takarar shugaban kasa na NDC.

Rabiu Kwankwaso ya kare Peter Obi

A hirar, tsohon gwamnan Kano ya ce a ganinsa Sheriff bai yi wadannan kalamai bisa hakikanin yanayin siyasa ba, illa kawai yana kokarin nuna biyayya ga masu mulki.

Ya ce:

"Na ji abin da ya fada lokacin da yake nan. Abin da yake nema shi ne ya burge dan'uwanmu da ke Villa domin ya nuna masa cewa yana aiki."

Kwankwaso ya kuma yi watsi da ra'ayin Ali Modu Sheriff game da siyasar Kano, yana mai cewa har yanzu tasirinsa a jihar yana nan daram.

Kwankwaso ya ce Obi ya gwada kwajinsa a siyasar Arewa a 2023
Obi, Henry Seriale Dickson jagoran NDC na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Ya ce:

"Ko babban makiyina zai gaya maka cewa Kwankwaso yana da Kano. Amma abin da yake son nunawa shi ne Kano ta rabu. Ni ba na cikin 'yan siyasar da ke taƙama. A mafi yawan lokuta ma ina farin ciki idan mutane sun raina abin da zan iya yi, saboda hakan yana sa su yi barci alhali kai kana aiki."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Obi ya kafa tarihi a Arewa - Kwankwaso

Kwankwaso ya ce yanayin siyasar jihar Kano da daukacin Arewacin Najeriya ya sha bamban da yadda Ali Modu Sheriff ya bayyana shi.

Ya kara da cewa:

"Zan iya tabbatar maka, da yardar Allah, mutanen Kano da na Arewacin Najeriya sun sha bamban da hoton da yake kokarin bayyana su."

Tsohon gwamnan ya kuma jaddada cewa Peter Obi ba sabon fuska ba ne a siyasar Arewa, yana mai tunatar da irin rawar da ya taka a zabukan baya.

Makusancin Kwankwaso na ganawa da APC

A wani labarin, kun ji cewa a karo na biyu a 'dan tsakaninnan, Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya gana da Sanata Rufai Hanga, wanda daya ne daga cikin manyan Kwankwasiyya a Kano.

Amma a wannan zaman, an hada har da mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Barau I Jibrin a babban birnin tarayya Abuja jim kadan bayan ya gana da gwamnann jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Wannan na zuwa ne yayin da lamari ke kara tsami a tsakanin tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rufa'i Hanga da ke ganin an i masa ba dai-dai ba, sannan ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya iya barin NDC idan an kore shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng