NDC, ADC, APC da Sauran Rigimar cikin Gida da ke Damun Jam'iyyun Siyasa a Kano
Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara zafi, wasu manyan jam'iyyun siyasa a jihar Kano na fuskantar rikice-rikicen cikin gida da suka shafi shugabanci, rabon madafun iko da zaɓen 'yan takara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Manyan jam'iyyun adawa ADC da NDC a jihar Kano su ne a kan gaba wajen rikice-rikicen cikin gida, wanda har ya kai ga zuwa kotu.
Daga cikin abubuwan da ke damun jam'iyyun akwai maganar shugabanci, musamman a jam'iyyar ADC, yayin da batun takara ya dabaibaye dukkanin jam'iyyun biyu.

Source: Facebook
Ita ma jam'iyyar APC na fama da na ta kalubalen, musamman ta fuskar maganar takarar Sanatan Kano da Tsakiya da aka ba wa Malam Ibrahim Shekarau.
Rikice-rikicen da ke jam'iyyu a Kano
Manyan jam'iyyu uku da aka tabbatar su na fama da rikicin cikin gida ta fuskoki da dama akwai hadakar yan adawa ta ADC, NDC ta su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da APC.
Ga jerin jam'iyyun da matsalolin da suka sakosu a gaba:
1. NDC
NDC ita ce jam'iyyar da ta fi bayyana rikicin cikin gida a Kano a halin yanzu. Rikicin ya samo asali ne daga zargin cewa an ƙwace tsarin jam'iyyar daga hannun waɗanda suka kafa ta bayan shigowar ƙungiyar Kwankwasiyya.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar sun yi zargin cewa an ware su daga yanke hukunci da kuma rabon mukamai.

Source: Facebook
Har ila yau, Sanata Rufa'i Sani Hanga ya fito fili yana bayyana rashin jin daɗinsa kan wasu matakan da aka ɗauka a cikin jam'iyyar, lamarin da ya ƙara nuna akwai sabani tsakanin shugabannin NDC a Kano.
Zuwa yanzu, gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda sun gana da Hanga, kuma ana ganin suna kokarin janye shi ne daga NDC.
Akwai sabanin da aka samu a jam'iyyar a sakamakon ba Mustapha Rabiu Kwankwaso takara sannan ga batun zargin rashin jituwa tsakanin Kwankwasiyya da shugabannin NDC na kasa.

Kara karanta wannan
Ana shirin zaben 2027, an ruguza lissafin APC a Amurka, Birtaniya da wasu kasashen waje
2. ADC
Jam'iyyar ADC ma na fuskantar saɓani a Kano, inda aka samu rashin jituwa tsakanin wasu shugabanni da fitattun mambobi.
Daya daga cikin fitattun muryoyin da suka bayyana damuwa ita ce Hajiya Naja'atu Muhammad, wadda ta yi suka kan wasu matakai da ake ɗauka a cikin jam'iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito a kwanakin baya cewa Naja'atu wacce ke shugabancin jam'iyyar a matakin shiyya ta ziyarci jihar Kano ta kuma sanar da rushe shugabancinta da soke takarar Sheikh Ibrahim Khalil.
A zantawarsa da majiyar Legit, dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam'iyyar, Balarabe Rufa'i ya ce yanzu haka ita kanta Hajiya Na'atu Muhammadu ba ta san matsayinta a ADC ba.
A kalamansa:
"Ita kan ta ba ta san mene ne matsayinta a jam'iyyar ba. Abin da ta yi da abin da Nafi'u Bala ya ke yi, ba su da wani banbanci, don raba kan al'umma ne."
"Saboda haka gaskiya mutane su sani ba ta da hurumi, kuma a halin yanzu da ake cikin jam'iyyar nan, ita kanta ba ta san matsayinta ba."
3. APC
Duk da cewa rikicin APC a Kano bai fito fili kamar na wasu jam'iyyu ba, ana ci gaba da samun takun saka tsakanin magoya bayan tsohon gwamna Ibrahim Shekarau da na Abdulsalam Abdulkarim (AA) Zaura.
Sabani ya ƙara bayyana bayan wasu 'yan takara suka amince da Shekarau a matsayin ɗan takarar sulhu na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, yayin da AA Zaura ya nuna cewa ba a gayyace shi taron sulhun da aka yi ba.

Source: Twitter
Jaridar The Guardian a baya ta ruwaito cewa wannan ya haifar da zanga-zanga daga magoya bayansa da kuma kiraye-kirayen a sake duba tsarin sulhun.
Amma rahotanni a ranar Juma'a sun nuna cewa Malam Ibrahim Shekarau ya kai ziyara kai tsaye wajen AA Zaura, duk da babu bayanan dalilin taron, ana ganin yana da nasaba da maganar takara.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kokari wajen sasanta rikicin da suka nemi su taso a jam'iyyar APC.
Kano: Jigon APC juya wa Tinubu baya
A baya, kun samu labarin cewa jagora a jam'iyya mai mulki ta APC a Kano, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda, ya ce ba ya goyon bayan tikitin Muslim-Muslim a 2027 kuma ba a isa a yaudare su ba.
Ya bayyana hakan duk da jam'iyyarsa ta koma kan tsohon tsarin Muslim Muslim da ya kawo gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mulkin a 2023, su na da wanda ake ganin shi Arewa ke bukata ya yi mulki.
AbdulMajid 'dan Bilki Kwamanda wanda ya dade yana fafutukar tara masu dangwala kuria'a a APC ya bayar da tababcin cewa a wannan lokacin Alhaji Atiku Abubakar na ADC za su zaba a 2027.
Asali: Legit.ng


