2027: Matasan Najeriya Sun Tafi Abuja domin Hada Atiku da Obi Su Kwarfe Tinubu
- Ɗaya daga cikin jagororin tafiyar Tinubu Must Go, Abba Hikima, ya ce za su gana da manyan ’yan takarar adawa domin neman su haɗa kai a zaɓen 2027
- Hikima ya ce manufarsu ita ce a ajiye bambance-bambancen siyasa gefe domin samar da haɗin gwiwar da zai fafata da Shugaba Bola Tinubu
- Ya bayyana cewa za su gabatar da wannan buƙata ne a madadin dimbin magoya bayan tafiyar TMG da ke neman a haɗa kan ’yan adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗaya daga cikin jagororin tafiyar Tinubu Must Go, Abba Hikima, ya bayyana cewa zai gana da manyan ’yan takarar adawa domin neman su haɗa kai gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da magoyo bayan 'yan siyasa ke cigaba da tallata gwanayensu domin ganin sun samu nasara a zaben 2027.

Source: Facebook
Abba Hikima ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a Facebook tare da wani bidiyonsa a filin jirgin sama.
Za a gana da 'yan adawa
Abba Hikima ya ce zai gabatar da buƙatar ne a madadin dimbin magoya bayan tafiyar Tinubu Must Go domin manyan ’yan adawa su yi aiki tare a zaɓen 2027.
Ya ce saƙonsu a bayyane yake, wato a ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu gefe, a haɗa kan ’yan adawa sannan a samar da ƙawance guda.
Lauyan ya bayyana cewa wannan ne abin da suke son gabatar wa manyan ’yan takarar adawa a ganawar da zai yi da su.
Mutane da dama sun dade suna kira ga Peter Obi da Atiku Abubakar da su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin samar da haɗin gwiwar siyasa, amma har yanzu ba a samu irin wannan haɗin kai ba.
A cewar Hikima, tafiyar TMG na son ganin an samar da matsaya guda tsakanin manyan ’yan adawa gabanin zaɓen.

Source: Facebook
Gargadi ga Atiku da Obi
Dan jarida, Jafar Jafar, ya wallafa a X cewa ’ya kamata yan siyasar Najeriya su koyi darasi daga zaɓen 2023, musamman kan tasirin rabuwar ’yan adawa.
Jafar ya bayyana cewa darasin da ya fito fili daga zaɓen 2023 shi ne bukatar ’yan adawa su haɗa kai, su ajiye burinsu na kashin kansu gefe sannan su samar da ƙawancen da zai iya kalubalantar jam’iyya mai mulki.
Ya ce a halin yanzu ’yan adawa na ci gaba da rarrabuwa yayin da kowanne ke bin abin da ya shafi muradinsa.
Tarkon Wike ga Atiku da Obi
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda gwamnonin G-5 suka tsara wata dabara da ta yi tasiri kan takarar shugaban ƙasa ta Atiku Abubakar na PDP a Kudu a 2023.
Wike ya ce G-5 ta yi la’akari da ƙarfin PDP a yankin da kuma yiwuwar Atiku samun ƙuri’u masu yawa, sannan ta bar Peter Obi na LP ya samu nasara a wasu jihohi kamar Edo da Cross River.
Ya ce G-5 ta kuma hana Obi samun nasara a Rivers saboda damuwar cewa nasararsa a jihar za ta iya aika wani saƙon siyasa da ba sa so, inda ya bayyana cewa gwamnonin sun yi hakan ne bisa dabarar da suka tsara.
Asali: Legit.ng

