2027: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Shi da Obi ke Shirin Magance Rashin Tsaro

2027: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Shi da Obi ke Shirin Magance Rashin Tsaro

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsokaci a kan tanadin da su ke yi wajen magance matsalolin rashin tsaro a Najeriya idan sun ci zabe
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin rashin tsaro da su ka hada da garkuwa da mutane da ayyukan ta'addanci da tsageru
  • Kwankwaso ya sako masu tayar da kayar baya da sauran 'yan bindiga a cikin tsarin da su ka shirya amfani da shi wajen kawar da rashin tsaro a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Abokin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa idan jam'iyyarsu ta samu nasara a zaɓen 2027, za a duba matsalar tsaro da kyau.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi yadda za ta kawo karshen mulkin Tinubu a 2027

Ya bayyana cewa a shirye su ke su tattauna da kowa, har da 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuffuka, domin nemo hanyar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya

Kwankwaso ya ce za su yi aiki wajen magance rashin tsaron Najeriya
Peter Obi, tutar NDC da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto" Mr. Peter Obi/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Channels Television a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2026.

Kwankwaso ya magantu kan rashin tsaro

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Kwankwaso ya ce mutane da dama da ke zaune a yankunan da ake fama da hare-haren 'yan ta'adda sun san waɗanda ke aikata laifukan da kuma wuraren da suke buya.

A cewarsa:

"Idan ka je yankunan da ake fama da rashin tsaro, zan iya gaya maka cewa mutane sun san kusan komai. Sun san inda suke, sun san sunayen waɗanda ke da hannu a lamarin."

Kwankwaso ya ce duk da cewa jama'a na da muhimman bayanai, da yawa daga cikinsu suna tsoron sanar da hukumomin tsaro saboda irin abubuwan da suka faru a baya.

Ya ce:

"Mutane da yawa sun taɓa ba jami'an tsaro bayanai a baya, amma ba su samu sakamakon da ya dace ba. Wannan ne ya sa yanzu suke jin tsoron fitowa su faɗi abin da suka sani."

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Alkawarin Kwankwaso kan tsaro

Saboda haka, ya ce gwamnatin NDC za ta fara ne da dawo da amincewar jama'a ga hukumomin tsaro domin su riƙa ba da bayanai ba tare da fargaba ba.

Kwankwaso ya ƙara da cewa gwamnati za ta kuma yi ƙoƙarin tattaunawa da 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuffuka domin a janye su daga ayyukan ta'addanci da tashin hankali.

Kwankwaso ya ce ba a za a yi watsi da batun aiki da karfin soja a kan yan ta'adda ba
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi ga manema labarai Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A cewarsa:

"Za mu yi aiki da mutane, har da 'yan ta'adda da masu aikata laifuffuka, domin mu ga abin da za a iya yi wajen hana su ci gaba da waɗannan ayyuka."

Sai dai ya jaddada cewa wannan ba yana nufin gwamnati za ta yi watsi da amfani da ƙarfin soji ba wajen kawo karshen ta'adadanci a Najeriya.

An yi magana kan tikitin Obi, Kwankwaso

A baya, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NDC, Buba Galadima ya ce ana fuskantar ƙalubale wajen tabbatar da tikitin haɗin gwiwar tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gano abin da ake bukata don rage talauci a Najeriya

Ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan bayanan da ya yi a baya game da dalilan da suka jawo aka hada kai tsakanin manyan yan siyasar yayin da su ke kokarin ceto Najeriya ta hanyar kayar da Bola Tinubu.

Injiniya Buba Galadima ya kuma buƙaci a daina ɗora wa Peter Obi laifin juyin mulkin soja na shekarar 1966 da aka yi a kasar nan saboda ba hannunsa, kuma a daina tuna aya idan ana son a ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng