Rikicin bayan Zaben Fitar da Gwani Ya Raba kan APC a Jihar Niger
- Rikicin cikin gida na APC a jihar Neja ya kara tsananta bayan zaben fidda gwani, inda ake zargin Gwamna Mohammed Umaru Bago da dora 'yan takara
- Wannan al'amari ya jawo rashin jituwa da ya haifar da ficewar wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar zuwa ADC na jam'iyyar hamayya ta 'yan adawa
- Magoya bayan tsohon gwamna Abubakar Sani Bello sun kafa kungiyar NRM, tare da bayyana goyon bayansu ga dan takarar ADC domin kalubalantar Gwamna Bago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Neja ya kara kamari bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.
Rahotanni sun nuna cewa zargin da ake yi wa Gwamna Mohammed Umaru Bago na dora 'yan takara ya haddasa rashin gamsuwa a tsakanin mambobin jam'iyyar, inda wasu suka fara ficewa daga APC.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa majiyoyi sun shaida cewa da dama daga cikin wadanda suka ji an ware su sun ce tsarin zaben bai yi adalci ba, kuma bai mutunta dimokuradiyyar cikin gida ba.
'Yan jam'iyyar APC sun balle a Neja
Daily Post ta wallafa cewa rashin jituwar ta kai ga kafa kungiyar NRM, wacce mafi yawan mambobinta magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ne.
Jagoran kungiyar kuma tsohon shugaban ma'aikatan tsohon gwamnan, Mikail Bmitosahi, ya sanar da cewa kungiyar ta hade da jam'iyyar ADC domin neman sauyi a jihar.
Ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da dattawa, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki a dukkan kananan hukumomi 25 na jihar.

Source: Original
A cewarsa, sun zabi ADC ne saboda suna ganin jam'iyyar tana ba da dama ga dimokuradiyya, hada kai da shugabanci mai anfani ga al'umma.
Bmitosahi ya zargi gwamnatin Bago da gaza magance matsalolin tsaro, rashin aikin yi, ilimi, lafiya, samar da ruwan sha da kuma hanyoyi.

Kara karanta wannan
Yan adawa sun yi wa gwamnati ca da ta ce ƴan ta'adda sun yi kuste cikin jami'an tsaro
Neja: Kungiyar NRM za ta zabi ADC
Ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta fara tattara magoya baya daga kowace karamar hukuma, gunduma da mazaba domin marawa ADC baya a zaben 2027. Daga cikin wadanda suka shiga kungiyar akwai tsoffin kwamishinoni Yusuf Suleiman, Usman Tinau da Mamman Musa.
A yayin wata ziyarar jaje da ya kai fadar Sarkin Kagara, Gwamna Bago ya zargi wasu magoya bayan tsohon gwamna Abubakar Sani Bello da kokarin kawo cikas ga gwamnatinsa.
Ya ce:
"Mutanen gwamnatin Abubakar Sani Bello da kwamishinoninsa da magoya bayansa ne ke yakar gwamnatina. Idan ina so zan iya bincikensa kamar yadda aka binciki gwamnatocin baya, amma na zabi hanyar zaman lafiya."
Sai dai rikicin bai tsaya nan ba, domin wasu 'yan takarar APC sun yi korafin cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani yadda ya kamata ba.
Sanata Mohammed Bima ya ce sun mika koke ga shugabancin APC na kasa, yana gargadin cewa za su dauki matakin da suka dace idan ba a warware korafinsu ba.
An sa takunkumi a jihar Neja
A baya, mun kawo labarin cewa gwamnatin jihar Neja ta sanya dokar hana fita a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Rafi bayan barkewar sabon rikicin kabilanci tsakanin Kamuku da Fulani.
Gwamna Umaru Bago ya ba hukumomin tsaro umarnin tura jami'ai da dukkan kayan aiki zuwa yankunan da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya da hana sake barkewar rikici a jihar.
Bago, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta, ya umarci hukumomin tsaro da su yi amfani da dukkan tsarin tsaro da ke akwai a fadin yankunan da abin ya shafa,
Asali: Legit.ng

