'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Gwamnatin Tarayya Ta Sayo Sababbin Jiragen Yaki

'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Gwamnatin Tarayya Ta Sayo Sababbin Jiragen Yaki

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sanya hannu kan wani muhimmin yarjejeniya da Bell Textron na Amurka domin ci gaba da shirin sayen jiragen yaƙi 12 na AH-1Z Viper.
  • Babban hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce jiragen za su ƙara ƙwarewar aiki da ƙarfin rundunar wajen tunkarar barazanar tsaro
  • Matakin na daga cikin shirin Gwamnatin Tarayya na sabunta kayan aikin rundunar soji da ƙarfafa tsarin tsaro da kariyar ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ɗauki wani muhimmin mataki na sayen jiragen yaƙi masu saukar ungulu guda 12 na AH-1Z Viper, bayan gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanin Bell Textron a Amarillo, Texas, Amurka.

Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ne ya jagoranci tawagar rundunar zuwa bikin, wanda ya zama wani muhimmin mataki wajen aiwatar da shirin haɗin gwiwar tsaro tsakanin Gwamnatocin Najeriya da Amurka.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Dalilin da ya sa Tinubu ya ki zuwa Amurka, ya tura Shettima taron UNGA

Najeriya ta sayo sababbin jiragen yaki
Tawagar Najeriya tare da ta kamfanin Amurka Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Facebook

Za a ƙarfafa ƙarfin rundunar

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026 a shafin Facebook.

A cewar sanarwar, sayen jiragen na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sabunta Rundunar Sojin Najeriya. Ya ce shirin zai kuma taimaka wajen ƙarfafa tsarin tsaro da kariyar ƙasa.

Da yake jawabi a bikin, Aneke ya ce sayen jiragen zai ƙara inganta ƙwarewar Rundunar Sojin Najeriya wajen gudanar da ayyukanta.

Jiragen za su taimaka wajen ayyukan tsaro

Babban Hafsan Sojin Sama ya ce shirin ya yi daidai da manufar jagorancinsa ta gina rundunar da ke da ƙwarin gwiwa da ƙwarewa, wadda za ta iya amfani da ƙarfin jiragen sama yadda ya kamata tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa. Ya ce hakan zai taimaka wajen cimma manufofin tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke kwamandojin 'yan ta'adda da ke da hannu a kisan babban janar a Katsina

Aneke ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kayan aikin da ake saye sun haifar da ingantaccen sakamako a fagen yaƙi da sauran ayyukan tsaro.

Aneke ya gode wa Tinubu

Aneke ya nuna godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin “jagoranci mai ma’ana, goyon baya mara yankewa da jajircewa wajen ƙarfafa tsarin tsaro da kariyar Najeriya.”

Ya ce irin wannan goyon baya na da muhimmanci wajen samar da kayan aikin da ake buƙata domin inganta ƙarfin Rundunar Sojin Sama.

An karɓi wasu sababbin jirage biyar

Wannan matakin ya zo ne kwanaki shida bayan Rundunar Sojin Sama ta karɓi wasu sababbin jirage masu saukar ungulu guda biyar.

An bayyana cewa karɓar jiragen na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sabunta ƙarfin rundunar ta sama da kuma ƙarfafa martanin Sojojin Najeriya kan barazanar tsaro.

Jiragen da aka karɓa sun haɗa da AW-109 Trekker B guda uku, waɗanda kamfanin Leonardo Helicopters na Italiya ya ƙera, da kuma H-125 guda biyu, waɗanda Airbus Helicopters ya ƙera.

An sayo jiragen yaki
Air Vice Marshal Sunday Aneke na sanya hannu a jikin jirgin yaki Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Facebook

Sojojin sama sun farmaki 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

Ta tabbata Tinubu ba zai je Amurka ba, ya ba Shettima umarni kan taron UNGA

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kai farmakin sama kan wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne a yankin Yankuzo, Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma ne suka kai farmakin ta hanyar yin amfani da jiragen yaki biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng