APC da PDP Sun Fara Saka Bayanan 'Yan Takarar Gwamna a Shafin INEC
- Babban jam'iyyar adawa ta PDP da jam'iyya mai mulki ta APC sun fara shigar da sunayen 'yan takararsu na gwamna da na majalisar jiha a shafin INEC gabannin zaben 2027
- Sakataren tsara ayyuka na PDP, Umar Bature, ya tabbatar da cewa sun fara aikin ne tun ranar Asabar kuma yana tafiya cikin nasara ba tare da wata matsala ba
- Rahoto ya nuna cewa jam'iyyar APC ta ba gwamnoninta 16 masu neman tazarce fifiko a matakin farko na tura bayanan zuwa shafin hukumar zabe ta kasa, wato INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam'iyyar adawa ta PDP da jam'iyya mai mulki ta APC sun fara gudanar da aikin shigar da sunayen 'yan takararsu na gwamna da na majalisun jiha a shafin yanar gizo na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Kara karanta wannan
Yan adawa sun yi wa gwamnati ca da ta ce ƴan ta'adda sun yi kuste cikin jami'an tsaro
Sakataren tsara ayyuka na jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Bature, ya bayyana cewa jam'iyyar ta fara shigar da sunayen ne tun ranar Asabar.

Source: Twitter
Wani babban jami'in jam'iyyar APC ya tabbatar wa Punch cewa jam'iyyar ta fara daurawa INEC sunayen 'yan takarar da kwamitin sauraron ƙoke-ƙoke da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) suka amince da su.
Tsarin PDP da PDP ke bi
A wata tattaunawa ta musamman, Umar Bature ya bayyana cewa aikin daurawa INEC bayanan 'yan takara yana tafiya cikin tsari mai kyau kuma za su kammala kafin wa'adin 8 ga Agustan 2026.
Ya bayyana cewa:
"Jam'iyyar PDP ta fara daurawa ma'aikatar INEC bayanan 'yan takarar gwamna da na majalisun jiha tun ranar Asabar.
"Aikin yana tafiya cikin sauƙi ba tare da wata matsala ta na'ura ba, kuma muna da kyakkyawan zaton cewa za mu kammala kafin wa'adin da aka gindaya."
Gwamnonin APC masu son tazarce
A gefe guda, majiyar jam'iyyar APC ta bayyana cewa tana ba gwamnoninta 16 masu neman komawa kan karaga fifiko a tsarin shigar da sunayensu.
Gwamnonin sun hada da Umo Eno (Akwa Ibom), Hyacinth Alia (Benue), Uba Sani (Kaduna), Abba Yusuf (Kano), Dikko Radda (Katsina),
Sauran sun hada da Nasir Idris (Kebbi), Umaru Bago (Niger), Caleb Mutfwang (Plateau), Ahmed Aliyu (Sokoto), Agbu Kefas (Taraba) da Dauda Lawal (Zamfara).
Haka zalika, jerin sunayen na APC zai ƙunshi sabbin 'yan takara 12, da suka hada da Obafemi Hamzat (Lagos), Solomon Adeola (Ogun), Kingsley Chinda (Rivers), Eric Opah (Abia).
Mohammed Abubakar (Bauchi), Mustapha Gubio (Borno), Jamilu Gwamna (Gombe), Ahmed Wadada (Nasarawa) da Baba Malam Wali (Yobe) na cikinsu.

Source: Facebook
Jaridar Business Day ta wallafa cewa ana sa ran jam'iyyun siyasa za su ɗaura sunayen 'yan takarar gwamna 28 da na majalisar jiha 993.
Jam'iyyu 3 da suka makara
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyun siyasa guda uku sun kasa ɗaurawa INEC sunayen 'yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimaka kafin kulle shafin hukumar.
Wani babban jami'in INEC ya bayyana cewa jam'iyyun da abin ya shafa sun haɗa da APGA da ɓangaren PDP ƙarƙashin Nyesom Wike.
Haka zalika akwai ɓangaren jam'iyyar LP ƙarƙashin Nenadi Usman, duk da cewa kusan dukkan sauran jam'iyyun sun kammala nasu cikin nasara.
Asali: Legit.ng

