Shugaban APC Ya Gana da na Hannun Daman Kwankwaso, Sanata Kabiru Gaya

Shugaban APC Ya Gana da na Hannun Daman Kwankwaso, Sanata Kabiru Gaya

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar girmamawa ga Sanata Kabiru Gaya da ke jam'iyyar NDC a Kano
  • Yilwatda ya ce sun tattauna kan haɗin kan Jihar Kano, yana mai jaddada cewa shugabanni su fifita muradun al'umma fiye da bambancin siyasa
  • Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Kabiru Gaya bai fitar da wata sanarwa a hukumance da ke nuna cewa zai koma jam'iyyar APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar girmamawa ga wani jigo na jam'iyyar NDC a Kano, Sanata Kabiru Gaya.

Yilwatda ya bayyana cewa tattaunawar da suka yi ta fi mayar da hankali ne kan haɗin kan al'ummar Kano da kuma buƙatar shugabanni su ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi yadda za ta kawo karshen mulkin Tinubu a 2027

Sanata Kabiru Gaya da Nentawe Yilwatda
Nentawe Yilwatda bayan ganawa da Sanata Kabiru Gaya a Abuja. Hoto: Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce dimokuraɗiyya na ƙara ƙarfi ne idan shugabanni sun fifita muradun jama'a sama da bambancin siyasa.

Abin da shugaban APC ya ce

Yilwatda ya bayyana Kabiru Gaya a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC, duk da cewa yanzu yana cikin jam'iyyar NDC.

Ya ce:

"A yau na kai ziyarar girmamawa ga Sanata Kabiru Gaya, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa babbar jam'iyyarmu ta APC, wanda yanzu ya koma NDC.
"Tattaunawarmu ta kasance cikin yanayi mai kyau kuma ta mayar da hankali kan haɗin kan Jihar Kano. Mun amince cewa shugabanni na da alhakin ƙarfafa tattaunawa da zaman lafiya.
"Dimokuraɗiyya ba ta ƙarfafa ta hanyar rarrabuwar kai ba, sai dai idan muka haɗa kai wajen fifita muradun jama'a sama da bambancin siyasa."
Sanata Kabiru Gaya da Nentawe Yilwatda
Shugaban APC yana tattaunawa da Sanata Kabiru Gaya. Hoto: Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Me ya faru kafin ziyarar?

Kara karanta wannan

Sanata na hannun daman Kwankwaso ya sa labule da shugaban APC da Barau

Ziyarar Kabiru Gaya ta zo ne sa'o'i kaɗan bayan shugaban APC ya gana da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma wani jigo na NDC, Sanata Rufai Hanga.

Yilwatda ya ce tattaunawar da suka yi ta shafi ci gaban Kano da kuma hanyoyin ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar haɗin kan shugabanni.

Kabiru Gaya na daga cikin manyan 'yan siyasar Kano da ke aiki tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ke takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar NDC a zaɓen 2027.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Kabiru Gaya da ke nuna cewa zai fice daga NDC ko kuma ya koma jam'iyyar APC.

Me yasa ake sauya sheka?

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya danganta yawaitar sauya sheƙar 'yan siyasa da rashin ingantacciyar akida.

Ganduje ya ce rashin tsayayyun manufofi a jam'iyyu ya sa 'yan siyasa ke sauya sheƙa saboda muradun kansu maimakon bin ƙa'ida ko akida.

Ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wani littafi a Abuja, inda ya ce wannan matsala na ci gaba da haifar da sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng