Ana Shirin Zaben 2027, An Ruguza Lissafin APC a Amurka, Birtaniya da Wasu Kasashen Waje

Ana Shirin Zaben 2027, An Ruguza Lissafin APC a Amurka, Birtaniya da Wasu Kasashen Waje

  • Babbar Kotun Abuja ta rusa dukan rassan jam'iyyar APC da ke Birtaniya, Amurka da sauran kasashen waje
  • Kotu ta ce babu wata jam'iyyar Najeriya da ke da ikon kafa reshe a kasashen waje, inda ta umarci APC ta mika sama da Naira miliyan 30 da ta tara
  • A cewar kotun da ke Abuja, masu gudanar da rassan jam'iyyu a ketare na iya fuskantar tara da ɗaurin kurkuku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Abuja da ke Maitama ta rusa rassan jam'iyyar APC da ke Birtaniya, Amurka da sauran kasashen waje, inda ta bayyana cewa sun sabawa doka.

Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya yanke hukuncin a karar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shigar, domin warware ce-ce-ku-cen da aka dade ana yi kan halaccin rassan jam'iyyun siyasar Najeriya a kasashen waje.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara taso Najeriya a gaba game da kare rayukan kiristoci

Nentawe.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyya mai mulki a Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Kotu ta umarci APC ta mika N30m

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kotun ta kuma umarci APC ta mika sama da Naira miliyan 30 da aka tara daga sayar da fom ga INEC.

Mai shari'ar ya ce jam'iyyar APC mai mulki ba ta da ikon tara irin wadannan kudade a wajen iyakokin Najeriya.

Ya ce:

"Jam'iyyar da ake ƙara ta farko ba ta da ikon kafa, gudanarwa, amincewa, sa ido ko kuma karbar kudade daga membobinta da ke wajen iyakokin Tarayyar Najeriya."

Kotun ta kuma bayyana cewa duk wata jam'iyyar siyasa dole ne ta sanar da INEC tare da bayyana duk wata gudummawar kudi da ta samu daga kasashen waje cikin kwanaki 21, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Haramun ne kafa rassan jam'iyyu a ketare

Kotun ta yanke cewa babu wata doka da ta amince da kafa rassan jam'iyyun siyasar Najeriya a kasashen waje.

Kara karanta wannan

A karshe, INEC ta yi matsaya kan takarar Atiku da 'yan ADC a 2027

Sai dai ta bayyana cewa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje na da 'yancin mara wa 'yan takararsu baya ko gudanar da yakin neman zabe, amma ba za su iya kafa ko gudanar da reshen jam'iyya ba.

Haka kuma kotun ta ce jam'iyyun siyasa ba su da ikon shirya ko gudanar da tarukan jam'iyya ga 'yan Najeriya da ke zaune a ketare.

APC Nigeria.
Tutar jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Hukuncin kafa rassan jam'iyyu a waje

Mai shari'ar ya kara da cewa duk wanda ya kafa ko ya jagoranci reshen wata jam'iyyar siyasa ta Najeriya a kasashen waje, ko kuma ya rika karbar kudin rajista da gudummawa, ya aikata laifi.

A cewarsa, irin wannan laifi na iya jawo tarar Naira miliyan biyar tare da hukuncin ɗaurin kurkuku, kamar yadda Guardian ta rahoto.

An rusa dukkan rassan APC na ketare

Kotun ta umarci APC da ta rusa dukkan kwamitocin gudanarwa da shugabannin jam'iyyar da ke Birtaniya da sauran kasashen waje.

Haka kuma ta haramtawa jam'iyyar kafa ko ci gaba da gudanar da duk wani reshe a wajen iyakokin Najeriya.

Shugaban APC ya gana da sanatan Kano

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufai Sani Hanga na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana tilasta wa ɗan jarida fallasa majiyoyinsa a shari'ar Ganduje

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan tayin da APC ta yi wa Sanatan na ya sauya sheka zuwa cikinta daga jam'iyyar NDC.

Yilwatda ya ce ganawa da Sanata Hanga ta gudana cikin mutunta juna, inda suka fi mayar da hankali kan jin daɗin al'ummar Kano maimakon bambancin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262