Hukumar Alhazai Ta Sanar da Kudin Kujerar Hajjin Shekarar 2027 a Jihar Kano
- Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da cewa ta amince da Naira miliyan 7 a matsayin kudin kujerar hajjin 2027
- Bayan haka, hukumar ta kuma jaddada tsayar da 25 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar ƙarshe ta yin rajista
- Ta kara da cewa mahajjatan da ba su gabatar da fasfon ƙasashen waje ba na iya rasa gurbinsu na sauke farali a shekara mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da Naira miliyan 7 a matsayin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin badi na ƙarshe.
Hukumar ta kuma tabbatar da ranar 25 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar ƙarshe da mahajjata za su kammala rajista.

Source: Facebook
Leadership ta ce shugaban hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya fitar.

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027
Matawalle ya buƙaci waɗanda suka yi niyyar zuwa aikin Hajjin amma ba su kammala rajistarsu ba da su gaggauta yin hakan kafin cikar wa’adin.
Ya kuma jaddada cewa mahajjatan da ba su gabatar da fasfon ƙasashen waje na inganci ba su ɗauki matakin yin hakan cikin gaggawa.
Ba za a ƙara wa'adin rajista ba
Babban Daraktan ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta ƙara wa’adin rajistar da aka tsayar daga ranar 25 ga Agusta, 2026 ba.
Ya buƙaci mahajjata da sauran masu ruwa da tsaki su bi umarnin hukumar yadda ya kamata domin guje wa matsalolin da ka iya tasowa a lokacin ƙarshe.
A cewarsa, kammala dukkan matakan rajista cikin lokaci yana da muhimmanci domin hukumar ta samu damar kammala shirye-shiryen da suka wajaba kafin fara aikin Hajjin.
Matawalle ya ce:
“Duk wani mahajjaci mai niyyar zuwa Hajji da ya yi rajista amma bai gabatar da fasfon ƙasashen waje mai inganci ba kafin ko a ranar 25 ga Agusta, 2026, na iya rasa gurbin zuwa Hajji.”
An buƙaci mahajjatan Kano su yi shiri
Hukumar ta sake tabbatar da aniyarta ta samar da ingantaccen aiki da hidima ga mahajjatan jihar a lokacin aikin Hajji na gaba.
Matawalle ya ce ana ci gaba da gudanar da shirye-shirye domin tabbatar da cewa aikin Hajjin ya gudana cikin sauƙi da nasara.

Source: Facebook
Hukumar ta ce bin ƙa’idojin rajista tun da wuri zai taimaka wajen sauƙaƙa tsare-tsaren tafiya da kuma daidaita sauran harkokin aikin Hajjin.
Ta kuma ƙara tunatar da mahajjata cewa kammala rajista da gabatar da takardun da ake buƙata cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da samun gurbin Hajji.
NAHCON ta bukaci a fara biyan N5m
A wani rahoton, kun ji cewa NAHCON ta buƙaci masu niyyar Hajjin 2027 su fara biyan ajiyar Naira miliyan biyar domin tabbatar da gurabensu da sauƙaƙa shirye- shiryen tafiya.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce fara biyan kuɗin tun da wuri zai ba maniyyata damar tabbatar da samun gurbi daà rage musu nauyin biyan kuɗin Hajji.
Asali: Legit.ng
