Amurka Ta Kara Taso Najeriya a Gaba game da Kare Rayukan Kiristoci

Amurka Ta Kara Taso Najeriya a Gaba game da Kare Rayukan Kiristoci

  • Duk da turo dakaru da kai hare-hare wasu sassan Najeriya, Amurka ta ci gaba da matsa wa Najeriya lamba game da zargin kisan kiristoci
  • A wata ganawa da aka yi tsakanin jami'an gwamnatin Trump da mashawarcin shugaba Bola Tinubu kan tsarim, Amurka ta sake dago maganar
  • Ta ce dole ne a dauki wasu matakai da za su kare rayukan kiristoci a Najeriya a yayin da 'yan bindiga ke kai hari kan wanda suka ga dama a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Amurka ta bukaci Najeriya ta kara kaimi wajen kare al'ummomin Kiristoci daga hare hare tare 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda.

Haka kuma gwamantin kasar ta bukaci a hanzarta dawo da mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu zuwa gidajensu lami lafiya.

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Amurka ta kuma magana game da rayukan kiristoci a Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, shugaban Amurka Donald Trump Hooto; Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an bayyana wannan bukata ne yayin ziyarar da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Frank Garcia, ya kai Abuja.

Abin da ya kawo jami'an Amurka Najeriya

Jaridar Punch ta kawo laarin cewa a yayin ziyarar, Garcia ya gana da manyan jami'an gwamnatin Najeriya da suka hada da Karamin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye.

Haka kuma an gana Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede; Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi; Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani; da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, an ce ziyarar ta mayar da hankali ne kan karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a bangarorin tsaro, kare Kiristoci da gyaran bangaren shari'a.

Haka kuma an kara mayar da hankali a kan bunkasa tattalin arzikin dijital, kasuwanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

"Shin Rasha ta kashe sanatan Amurka"; An fara nuna yatsa kan mutuwar aminin Trump

Kiran Amurka ga Najeriya

Sanarwar ta ce Garcia ya yaba da irin kokarin da Najeriya ke yi a karkashin Kwamitin Hadin Gwiwar Amurka da Najeriya domin magance batun sanya Najeriya cikin jerin kasashen da Amurka ke ce ana muzguna wa kiristoci.

Amurka ta yaba da kokarin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu Donald Trump na Amurka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Donald J Trump
Source: Getty Images

Sai dai ya bukaci gwamnatin Najeriya ta kara himma wajen kare Kiristoci daga hare-hare tare da ware karin albarkatu domin tabbatar da komawar 'yan gudun hijira gidajensu cikin tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa Garcia ya bayyana fatan samun karin ci gaba kafin taron gaba na Kwamitin Hadin Gwiwa da za a gudanar a birnin Washington DC a watan Agusta, inda za a tantance irin nasarorin da aka samu a bangarorin da aka amince a yi aiki tare.

Kiristoci sun karyata shugaban Amurka

A baya kun samu labarin cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa hare-haren da dakarun sojojin kasarsa suka kawo Najeriya sun sanya an daina kashe kiristoci a kasar.

Kara karanta wannan

Alaka ta munana: An hada baki da sojoji aka tsare dan majalisar Amurka a Isra'ila

Amma kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohin Arewa 19 da Abuja, ta fito ta yi martani ga shugaban kasar na Amurka, inda ta ce Trump ba ya samun bayanan da suka dace kan abubuwan da ke faruwa a zahiri.

Joseph Hayab ya soki maganar Trump, inda ya na ce kan cewa 'yan Najeriya, ba Kiristoci kaɗai ba, har yanzu ana ci gaba da kashe su da kuma yin garkuwa da su a jihohi da dama ba dare ba rana a gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng