Kaduna da Wasu Jihohi 12 da Za a Yi Mamakon Ruwa da Ambaliya daga Yau zuwa Kwanaki 7
- Hukumar NiMet ta yi gargadin yiwuwar ambaliyar bazata a jihohi 13 tsakanin 11 zuwa 20 ga watan Agusta, 2026
- Jihohin da ke cikin hadarin sun hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Kaduna, Kano da wasu jihohi da dama a fadin Najeriya
- Hukumar ta bukaci jama’a da hukumomin agaji su dauki matakan kariya tun da wuri domin kaucewa illar ambaliya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa ba tare da tsammani ba a jihohi 13 tsakanin ranakun 11 zuwa 20 ga Agusta, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa gargadin na da nufin taimakawa jama’a da hukumomin da abin ya shafa wajen shirye-shiryen tunkarar ambaliyar ruwa, daukar matakan gaggawa da rage illolin bala’i.

Source: Twitter
NiMet ta yi gargadin ne cikin wata sanarwar yanayi da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, 11 ga watan Agusta, 2027.
Jerin jihohin da NiMet ta yiwa gargadi
Hukumar ta ce jihohin da abin ya fi shafa sun hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Niger, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Plateau, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom.
NiMet ta ce hasashen ya yi la’akari da karfin ruwan sama da ake sa ran samu, danshin kasa, yanayin magudanan ruwa, tsarin kasa da kuma halayen madatsun ruwa.
Ambaliya na iya shafar al’umma
NiMet ta ce ambaliyar bazata na iya faruwa musamman a wuraren da ambaliyar ruwa ta saba faruwa, yankunan da suke kasa, birane da kuma al’ummomin da ke kusa da koguna.
Ta gargadi jama’a cewa ambaliyar na iya haifar da rufe hanyoyi, cunkoson ababen hawa da kuma kawo tsaiko ga harkokin sufuri.
Hukumar ta kuma ce ambaliyar na iya haifar da katsewar wutar lantarki da layukan sadarwa na wani lokaci.
Bugu da kari, ruwan sama mai karfi na iya rage gani, lamarin da zai iya kawo matsala ga zirga-zirgar ababen hawa da kuma harkokin sufurin jiragen sama.
An bukaci jama’a su yi hattara
Saboda haka, ta bukaci jama’a su rika bibiyar hasashen yanayi da gargadin ambaliya da NiMet da hukumomin kula da bala’o’i ke bayarwa.
NiMet ta shawarci jama’a da su guji tafiya da kafa ko tukin mota a kan hanyoyin da ruwa ya mamaye, gadoji da wuraren da ruwa ke gudana da karfi.

Source: Getty Images
Ta kuma bukaci mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliya ke iya shafa da su kasance cikin shiri, tare da yin tanadin komawa wuraren da suka fi aminci idan bukatar hakan ta taso.
Ambaliya ta yi barna a jihar Neja
A wani labarin, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta lalata kadarori da dama da darajarsu ta kaiNmiliyoyin Naira a wani sashe na rukunin gidajen Janar M.I. Wushishi da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.
Lamarin ya sa wasu mazauna yankin suka fice daga gidajensu domin tsira da rayukansu yayin da ruwa ya mamaye gidaje da dama.
Waɗanda lamarin ya shafa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta shiga tsakani tare da magance matsalar ambaliyar da kumaNabubuwan da ke haddasa ta a yankin.
Asali: Legit.ng

