Naja’atu: Munafuncin da ADC Ta Gani Ta Hana Ibrahim Khalil Takarar Gwamnan Kano

Naja’atu: Munafuncin da ADC Ta Gani Ta Hana Ibrahim Khalil Takarar Gwamnan Kano

  • Naja’atu Muhammad ta ce ba komai ya sa aka hana Ibrahim Khalil takara ba illa akidar da yake da ita a siyasa
  • ‘Yar siyasar ta yi bayanin hikimar zaben Ibrahim Amin Little ya yi wa ADC takarar gwamnan Kano a 2027
  • Mataimakiyar shugabar jam’iyyar ADC ta jefi Sheikh Khalil da zargin munafunci da rashin yarda da Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Naja’atu Muhammad ta yi karin haske game da abin da ya sa ADC ta ki tsaida Ibrahim Khalil a matsayin ‘dan takarar gwamna a jihar Kano.

Ganin shi ya yi takara sa'ilin da jam’iyyar ba ta da karfi a zaben 2023, wasu sun yi tunani Sheikh Ibrahim Khalil zai sake rike wa ADC tuta a jihar.

Ibrahim Khalil
Sheikh Ibrahim Khalil da ya yi takarar gwamnan Kano a ADC a 2023
Source: Facebook

A wani bidiyo da gidan rediyon Freedom ya daura a Facebook, an ji Hajiya Naja’atu Muhammad tana mai zargin Ibrahim Khalil da yi wa ADC manufunci.

Kara karanta wannan

APC ta karbe mutumiyar Atiku Abubakar da ta sauya sheka daga jam’iyyar ADC

Mataimakiyar shugabar ADC ta shiyyar Arewacin Najeriya ta yi ikirarin cewa malamin bai goyon bayan takarar Atiku Abubakar duk da suna tare.

‘Yar siyasar ta ce ‘dan takarar gwamnan na Kano a 2023 ya fifita Bola Ahmed Tinubu a kan Atiku Abubakar mai neman shugaban kasa a ADC.

"A ce ‘dan takarar gwamna bai yarda da ‘dan takarar shugaban kasarmu ba, ya fi yarda da Asiwaju.
"Ku fada mani dalilin da ya sa za mu bas hi takarar gwamna. Wannan shi ne magana, kar a dada, kar a kara."

- Hajiya Naja’atu Muhammad

Domin ta samu hujja a addinin Musulunci, ta soki munafunci har tana cewa an sauke sura guda a littafin Kur’ani domin a tona asirin munafukai.

“Don mun samu munafukai a ADC ‘normal’ ne, Allah ya shirye su.

‘Yar adawar ta bayyana cewa tun farko ba a samu yadda ake so ba wajen tsaida ‘dan takarar gwamnan Kano a ADC har ta lai lokaci ya kure.

Ganin lokacin da INEC ta ba jam’iyyu ya kure, sai ADC ta yi amfani da tsarin maslaha domin zabo wanda za a ba tuta kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar gwamna a PDP bai son tazarce ya ce wa’adi 1 rak ya ishe shi

Kamar yadda aka fi saninta, Naja’a ta ce ba a Kano ne kurum haka ta faru ba, an yi haka a sauran jihohi, Kano Live 24 ta wallafa bidiyon jawabinta.

Kwamitin ADC da ya tsaida 'dan takaran Kano

Dama can Majalisar NWC ta ADC ta kafa kwamiti da zai yi wannan aiki karkashin Sanata Ben Oni da ita Naja’atu Muhammad a matsayin sakatariyarsu.

Wannan kwamiti ya zauna da Ibrahim Amin Little da Ibrahim Khalil da mutanensu kuma aka yi yarjejeniya, a karshe aka yarda a tsaida mutum guda.

Hajiya Naja ta ce ba ita ta hana Khalil tutar takara ba, akwai sauran mutane shida a kwamitin da suka yi la’akari da karbuwa, yiwuwar cin zabe da adalci.

Haka kuma kwamitin da ya kunshi manyan ADC kamar su Aminu Tambuwal, Liyel Imoki da Abubakar Malami ya fi gamsuwa da akidar Alhaji Ibrahim Little.

Me Ibrahim Khalil ya ce kan Bola Tinubu?

Ga masu neman abubuwan da malamin addinin ya fada game da Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad ta bukaci jama’a su yi bincike a yanar gizo.

Ana zargin ‘dan siyasar ya taba cewa Tinubu ya fi dacewa da Najeriya a halin da ake ciki. Saboda irin wadannan maganganu ADC ta ji tsoron tsaida shi.

Kara karanta wannan

Kiran da Sheikh Maqary ya yi wa mabiya darika a jami'a a rigimar wazifa da ATBU

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng