Peter Obi, Kwankwaso, Binani da Fitattun ‘Yan Siyasa 10 da Suka Rabu da Hadakar ADC

Peter Obi, Kwankwaso, Binani da Fitattun ‘Yan Siyasa 10 da Suka Rabu da Hadakar ADC

Abuja - A shekarar bara ne ‘yan adawa suka fara yunkurin yin hadaka domin tunkarar jam’iyyar APC mai mulki idan an zo zaben 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A karshe jagororin hamayya da-dama sun ammince su shiga jam’iyyar ADC kansu a hade da nufin ganin bayan gwamnatin Bola Tinubu.

Sai dai bayan an yi wannan, daga baya an rika samun wasu manyan ‘yan siyasa da suka bar ADC, suka sauya-sheka zuwa wasu jam’iyyu.

'Yan ADC
Rabiu Musa Kwankwaso, Aisha Dahiru Binani da Peter Obi da suka bar ADC Hoto: Saifullahi Hassan/Ahmed Audijnr/Peter Obi
Source: Facebook

Wannan rahoto ya tattaro jerin ‘yan siyasar da ADC ta rasa a cikin shekarar nan. Sai dai babu mamakin akwai wasu da ba mu ambata ba.

'Yan siyasar da suka rabu da ADC

1. Peter Obi

A watan Mayun 2026 Peter Obi ya yi sallama da jam’iyyar ADC a lokacin ya fake da rigimar da ake yi Nafiu Bala da ya shigar da kara a kotu.

Kara karanta wannan

Dalilin Atiku na jawo Amaechi su yi takarar shugaban kasa tare a ADC ya fito fili

Reuters ta yi bayanin yadda Peter Obi suka faskara adawa gabanin zabe. Kamar yanzu da ya shiga NDC, a zaben 2023 ya yi raba kuri’u ne a LP.

2. Rabiu Musa Kwankwaso

Shi ma Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar ADC ‘yan kwanaki kadan bayan shi da wasu mutanensa sun rabu da NNPP mai adawa.

Tsohon gwamnan Kano ya bi Obi zuwa NDC ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, ADC ta ce son takara ta sa suka tafi inji Leadership.

3. Babachir David Lawal

Injiniya Babachir David Lawal wanda ya yi sakataren gwamnatin tarayya ya shiga jerin manyan ‘yan siyasar da suka raunana ADC a shekarar nan.

A zantawarsa da tashar Channels, Babachir ya ce ya rabu da jam’iyyar ne saboda magu-magu da aka yi wajen tsaida Atiku Abubakar takara.

4. Aisha Dahiru Binani

Tun a watan Afrilu aka rika rahoto cewa babu jituwa tsakanin magoya bayan Aisha Dahiru Binani da wasu ‘yan ADC a jihar Adamawa.

Bayan kusan makonni biyu, The Sun sai ta rahoto cewa ‘yar takarar gwamnan APC a zaben 2023 ta bar APC kuma ta shiga jam’iyyar NDC.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi yadda Kiristoci suka karbi tikitin Muslim Muslim a Najeriya

5. Elisha Abbo

Kamar dai Aisha Dahiru Binani, shi ma Sanata Elisha Abbo ya yi watsi da ADC zuwa LP. ‘Dan siyasar ya ce ‘yan hadaka sun jefa kansu cikin rikici.

TVC ta rahoto Abbo yana cewa zai fadi wanda zai goyi baya a 2023. Abin da ya fi daukar hankali shi ne a mahaifar Atiku Abubakar aka yi wannan.

Atiku Abubakar
Jagora kuma 'dan takaran ADC a Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

6. Leke Abejide

Kusan duk wanda ya shiga ADC a shekarar bara ko a 2026, ya iske Hon. Leke Abejide ne, tsohon ‘dan majalisa da har ya yi mata takarar gwamna.

Premium Times ta rahoto lokacin da ‘dan majalisar na Kogi ya rabu da ADC saboda rikicin gida. Daga baya kuma David Mark ya yi nasara a kan shi a kotu.

7. Salihu Lukman

A Kaduna, Salihu Luqman Muhammad ya yi ban-kwana da jam’iyyar hamayya ta ADC, ya zargi Nasir El-Rufai da fusata shi ya canza sheka.

The Nation ta ce Salihu Luqman ya sanar da David Mark cewa ya bar APC. Kafin nan ya rike mataimakin shugaban APC na kasa na shiyyar Arewa.

Kara karanta wannan

Pantami ya shirya wa 2027 da kyau, ya soma jefa wa APC maganganu a dunkule

8. Buba Galadima

Duk da ba mu da tabbacin Injiniya Buba Galadima ya taba karbar katin zama ‘dan ADC, amma ana sa shi cikin wadanda suka fice daga jam’iyyar.

Da tashi kawo rahoton wasu da suka sauya-sheka daga ADC, jaridar Business Day ta jero har da sunan babban na hannun daman Rabiu Kwankwaso.

9. Kabiru Marafa

Makonni uku da shigarsa ADC daga jam’iyyar APC, sai aka ga rahoto a jaridar Punch cewa tsohon sanatan Zamfara ta tsakiya ya tattara ya yi gaba.

Sanata Kabiru Marafa wanda shi ne shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu a Zamfara lokacin zaben 2023 ya shiga jam’iyyar NDC a Afrilu.

10. ‘Yan majalisa

Akwai Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da-dama da suka rabu da ADC saboda ganin iyayen gidansu a siyasa - Obi da Kwankwaso sun yi waje.

‘Yan majalisar da suka yi watsi da ADC

1. Yusuf Umar Datti

2. Sani Adamu (Wakil)

3. Zakari Umar Mukhtari

Kara karanta wannan

Abin da shugabannin jami’ar MAUN suka fada game da Nasa’i Gwadabe ya fito

4. Kamilu Ado

5. Harris Okonkwo

6. George Ozodinobi

7. Lilian Obiageli Orogbu

8. Peter Anekwe

9. Emeka Idu

10. Ifeanyi Uzokwe

11. Victor Afam Ogene

12. Thaddeus Attah

13. OluwaSeyi Sowunmi

14. George Olawande

15. Jesse Onuakalusi

16. Murphy Osaro Omoruyi

17. Umezuruike Manuchim

Sanatocin da suka rage a ADC da jam'iyyun adawa

An kawo maku rahoton yadda jam'iyya mai mulki ta APC ta mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, inda a halin yanzu sanatoci 20 kacal ne suka rage a adawa.

Yawancin sanatocin hamayyar sun bar jam'iyyunsu na asali (kamar PDP da LP) zuwa sababbin jam'iyyu ko wasu kananan jam'iyyun kamar ADC da NDC.

Wasu fitattun sanatoci sun bayyana cewa ba za su sake tsayawa takara a zabe mai zuwa ba, kamar Aminu Waziri Tambuwal da takawaransa Ibrahim Lamido.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng