Bauchi: Tsohon Kwamishina Ya Zama Mataimakin Dan Takarar Gwamna a APC
- Rahoto ya nuna cewa jam'iyyar APC ta zaɓi Farouk Mustapha a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna a jihar Bauchi a zaben 2027
- Farouk Mustapha ya taɓa zama kwamishinan ayyuka na musamman da raya karkara a gwamnatin jihar Bauchi karkashin Bala Mohammed
- Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC ya tabbatar da an riga an isar da sunan Mustapha ga hukumar zabe ta kasa (INEC) a birnin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyar APC a jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya zaɓi mataimaki.
Ya zabi tsohon kwamishinan ayyuka na musamman da raya karkara, Farouk Mustapha, a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa sakataren tsare-tsare na jihar na jam'iyar APC, Sallah Kafi, ne ya bayyana wannan labari ga manema labarai.

Kara karanta wannan
Gwamna Kefas ya ajiye mataimakinsa, ya zabi mace a matsayin abokiyar takara a 2027
APC ta dauki mataimakin gwamna
Sakataren APC ya yi magana yana mai cewa shugabancin jam'iyar tare da ɗan takarar sun riga sun kai sunan Mustapha da takardunsa zuwa ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato INEC, da ke birnin Abuja.
Kafi ya ce:
"Yanzu mun dawo daga Abuja bayan mun miƙa takardun, kuma an riga an rubuta sunan Farouk Mustapha a INEC a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a jihar Bauchi."
Murabus din da Mustapha ya yi
Daily Post ta wallafa cewa Mustapha ya kasance daga cikin kwamishimonin da suka yi murabus a gwamnatin Bauchi da Bala Mohammed ke jagoranta.
A baya, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ba da umarnin cewa duk waɗanda aka naɗa a siyasance kuma suna son tsayawa takara su bar mukamansu kafin ko a ranar 24 ga Afrilu 2027.
Bayan Mustapha ya bar ofis, ya kuma sanar da masu goyon bayansa da abokan siyasarsa da su yi haƙuri, yana alkawarin cewa zai sanar da su da zarar ya yanke shawara game da ƙungiyar siyasa da zai ci gaba da tafiya da ita.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Mataimakin shugaban APC da wasu manyan ƙusoshi sun fice daga jam'iyyar

Source: Twitter
Mustapha ya fita daga APM
Haka kuma, Mustapha ya yi murabus daga jam'iyyar APM, kafin ya shiga cikin tsarin zaɓe a ƙarƙashin APC mai adawa a jihar Bauchi.
Yanzu da aka gabatar da sunansa ga INEC, Farouk Mustapha ya zama ɗan takarar da zai yi wa Muhammad Abdullahi Abubakar mataimaki yayin neman zaɓen gwamnan jihar Bauchi a 2027, a ƙarƙashin jam'iyar APC.
Wannan mataki ya zo ne a lokacin da jam'iyun siyasa ke shirye-shirye sosai don babban zaben 2027 wanda ake sa ran zai dauki hankali jihar Bauchi.
Ana rikcici a APC a Bauchi
A wani labarin, mun kawo muku cewa mutanen tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar sun yi korafi kan zaben fitar da gwanin APC.
A wani taron manema labarai da suka yi, sun jaddada cewa jam'iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fitar da gwani da za a iya dogara da shi wajen fitar da 'yan takara ba.
A kan haka suka bukaci uwar jam'iyyar ta sake nazari kan zabar tsohon gwamnan Bauchi, Muhammad Abubakar a matsayin dan takararta na zaben 2027 a jihar.
Asali: Legit.ng