Rigima Ta Taso a APC bayan Sauya 'Yan Takara, 'Yan Jam'iyya Sun Fara Tutsu
- Daruruwan 'yan jam'iyyar APC sun yi zanga-zanga a Benue kan zargin sauya ɗan takarar majalisar wakilai da ya lashe zabe a baya
- Sun gudanar da zanga-zangar inda suka buƙaci a amince da Farfesa Iornem Kohol, wanda suka ce ya ci zaɓen fitar da gwanin da aka yi
- 'Yan jam'iyyar sun yi gargaɗin cewa watsi da sakamakon zaɓen fitar gwani zai saka dimokuraɗiyya da jam'iyyar cikin rudani a jihar Benue
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Daruruwan mambobin jam'iyyar APC daga Ƙananan Hukumomin Kwande da Ushongo na Jihar Benue sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Lessel, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ushongo,.
Sun buƙaci Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) na jam'iyyar ya mutunta sakamakon zaɓen fitar da gwani na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazabar Kwande/Ushongo.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa jama'ar yankin sun yi zanga-zangar ne bayan jam'iyyar APC ta sauya sunayen wasu 'yan takara sama da 20 a Najeriya.
Bukatar masu zanga-zangar APC
Masu zanga-zangar sun nace cewa Farfesa Iornem Kohol, wanda ake zargin ya lashe zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar ranar 16 ga Mayun 2027, shi ne ya kamata a amince da shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen 2027.
Sun yi watsi da rahotannin da ke cewa an bai wa ɗan majalisar mai ci, Terseer Ugbor, takardun tsayawa takara na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC).
An ce Farfesa Kohol ya lashe zaɓen fidda gwani ne da ƙuri'u 40,672, inda ya doke sauran 'yan takara biyar, ciki har da Terseer Ugbor wanda ya samu ƙuri'u 750.
Wadanda suka fita zanga-zangar
Jagororin zanga-zangar sun haɗa da Ken Kaase, Aondolumun Ordorugh da Fidelis na Mbakuha, waɗanda suka buƙaci shugabannin APC su martaba zaɓen fitar da gwani ta hanyar mutunta zaɓin da mambobin jam'iyyar suka yi.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Dalilin da ya sa APC ta sauya tsohon gwamna da sauran 'yan takara 25
The Sun ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun bayyana cewa sauya ɗan takarar ya saɓa wa muradin mambobin jam'iyyar, suna masu cewa ba ɗan majalisar mai ci suka zaɓa ba a zaɓen.

Source: Twitter
'Yan APC sun gargadi jam'iyya
Sun yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na yin watsi da sakamakon zaɓen zai raunana dimokuraɗiyyar a APC tare da rage amincewar mambobi ga tsarin zaɓen jam'iyyar.
Sun kuma kafa hujjar cewa ya kamata kujerar Majalisar Wakilan ta koma Ƙaramar Hukumar Ushongo, saboda Kwande ta riƙe kujerar na kusan shekara 20, yayin da Ushongo ba ta fitar da wakili ba tsawon shekara 16.
'APC ta kara karfi,' Gwamna Sule
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa a jam'iyyar APC na kara samun karbuwa a Najeriya.
Ya fadi haka ne yayin kaddamar da wasu ayyuka, inda ya ce kokarin da Bola Tinubu ke yi a jihar shi na kara sanya jama'a goyon bayan APC.
Abdullahi Sule ya alakanta nasarar da APC ta samu a zaben cike gurbin da aka yi a jihar da karbuwar jam'iyyar a wajen mutanen Nasarawa.
Asali: Legit.ng
