Jerin 'Yan Takara 26 da APC Ta Sauya Sunayensu bayan Zaben Fitar da Gwani
- Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya cire tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, da wasu 'yan takara 25 bayan zaben fitar da gwani
- Rahoto ya nuna cewa sauye-sauyen da jam'iyyar APC ta yi sun shafi 'yan takarar majalisar dattawa da na majalisar wakilai da dama
- A cikin wata takarda da ta fitar, APC ta ce sabon jerin sunayen da aka fitar ne za ta yi amfani da shi, kuma shi aka turawa hukumar INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamitin zartarwa na kasa (NWC) na jam'iyyar APC ya cire tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam, tsohon ɗan majalisar wakilai, Gbenga Elegbeleye, da wasu 'yan takara 24.
Waɗanda sauye-sauyen suka shafa sun haɗa da 'yan takarar kujerun majalisar dattawa bakwai da kuma 'yan takarar majalisar wakilai 19.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa an fitar da sauye-sauyen ne ta cikin wata wasiƙa da Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu tare, sannan aka miƙa wa INEC.
Dalilin sauya 'yan takarar APC
A cewar wasiƙar, sauya sunan 'yan takarar ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin daukaka kara na zaɓen fidda gwani ya bayar.
Wani ɓangare na wasiƙar ya ce:
“Bayan kammala sauraron ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani da aka gudanar kwanan nan, an duba rahotannin kwamitin daukaka kara, sannan NWC na APC ya amince da su a matsayin matsayar ƙarshe ta jam'iyyar kan mazaɓun da abin ya shafa.”
Sanatocin da APC ta sauya
A ɓangaren majalisar dattawa, Sanata Sunday Karimi ya maye gurbin Aro Samuel Bamidele a Kogi ta Yamma, yayin da Prince Paul Ikonne ya maye gurbin Edinburgh Uchenna Erondu a Abia ta Kudu.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
A Benue ta Arewa, Emmanuel Memga Udende ya karɓi tikitin da Gabriel Suswam ya rasa, yayin da Titus Tartenger Zam ya maye gurbin Benjamin T. Aber a Benue ta Arewa maso Yamma.
Shuaibu Isa Lau ya maye gurbin Mohammed Kabir Bello a Taraba ta Arewa, Adeniyi Adegbonmire ya maye gurbin Taiwo Fasoranti a Ondo ta Tsakiya, yayin da Olajide Ipinsagba ya karɓi tikitin Ondo ta Arewa daga hannun Gbenga Elegbeleye.

Source: Facebook
'Yan majalisar da APC ta sauya
A ɓangaren majalisar wakilai, jihar Benue ce ta fi samun sauye-sauye, inda mazaɓu biyar suka sauya 'yan takara.
Dickson Tarkighir ya maye gurbin Ikper Chris Terfa a Makurdi/Guma, Sesoo Ikpagher ya maye gurbin Livinus Tsar Adzor a Vandeikya/Konshisha.
Terser Ugbor ya maye gurbin Kohol Shedrach Iornem a Kwande/Ushongo, Sekav Dzua Iyortyom ya maye gurbin Gideon Inyom a Buruku, yayin da Austin Asema Achado ya maye gurbin Nongo David a Gwer.
A Taraba, Peter Abel Diah ya maye gurbin Sanusi Mohammed Galadima a mazaɓar Gashaka/Kurmi/Sardauna.
A Jihar Niger kuma, Abubakar Lado Abdullahi ya maye gurbin Adamu Tanko a Suleja/Tafa/Gurara, yayin da Adamu Suleiman ya maye gurbin Adamu Usman a Lavun/Edati/Mokwa.

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu
A Jihar Kwara, Raheem Tunji Olawuyi ya maye gurbin Olasumbo Florence Oyeyemi a mazaɓar Ekiti/Irepodun/Oke-Ero, yayin da Mohammed Mamman ya maye gurbin Bello Tauheed Abubakar a Edu/Patigi/Moro.

Source: UGC
Jihar Ondo ta samu sauye-sauye guda shida. Donald Ojogo ya maye gurbin Akingboye Leke a Ilaje/Ese-Odo, Festus Olarewaju ya maye gurbin Rasaq Obe a Idanre.
Oluwatimehin Akintomide ya maye gurbin Kayode Ijalana a Owo/Ose, Okunjinmi John Odimayo ya maye gurbin Olumuyiwa Daramola a Okitipupa/Irele.
Michel Olamidotun Akintomide ya maye gurbin Abiola Makinde a Ondo ta Yamma da ta Gabas yayin da Festus Ayodele Adefiranye ya maye gurbin Oyerinmade Matthew a Ile-Oluji/Oke-Igbo/Odigbo.
Sauran da APC ta sauya
Sauran sauye-sauyen sun haɗa da Abdulazeez Kaka wanda ya maye gurbin Samaila Abdu Suleiman a Kaduna ta Arewa, Samuel Okezie wanda ya maye gurbin Chris Nkwonta a mazaɓar Ukwa ta Gabas/Yamma a Jihar Abia.
Daily Nigerian ta wallafa cewa Ekumankama Joseph Nkama ya maye gurbin Iduma Igariwey Enwo a mazaɓar Afikpo/Edda ta Jihar Ebonyi.
ADC ta mikawa INEC sunan Atiku
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta daura sunan dan takarar shugaban kasar ta a shafin hukumar zabe ta kasa.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
Kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya sanar da cewa sun sanya bayanan Atiku Abubakar da Romiti Amaechi da zai masa mataimaki.
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ADC ta shirya ba 'yan Najeriya sabuwar kafar da za ta kawo sauyi a shugabanci a zaben 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng
