Matasa Sun Fito Farautar 'Yan Bindiga bayan Kashe Wani Jagoran Al'umma a Jihar Katsina

Matasa Sun Fito Farautar 'Yan Bindiga bayan Kashe Wani Jagoran Al'umma a Jihar Katsina

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kashe wani fitaccen jagoran al'umma a garin Gora da ke yankin karamar hukumar Malumfashi a Katsina
  • Wannana lamari ya fusata matasa a kauyukan Malumfashi, inda suka fito farautar yan bindigar da suka kashe dattijon
  • Rahotanni sun nuna akalla mutane bakwai sun jikkata kafin dakarun sojoji su kai dauki tare da kwantar da hankulan matasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Ana zargin wani hari da ‘yan bindiga suka kai ya haddasa barkewar rikici da ramuwar gayya a karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina.

An samu tashin hankalin ne a kauyukan Gora da ke gundumar Gorar Dansaka, Gidan Barau da ke gundumar Na’alma da kuma Gidan Maga da ke gundumar Dayi da misalin karfe 11:00 na safiyar Laraba.

Jihar Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta rahoto cewa mazauna yankin sun ce mutum bakwai sun jikkata, yayin da zirga-zirga ta tsaya na tsawon sa’o’i bayan fusatattun matasa sun toshe hanyar Gora.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka ɓarna, sun kashe mai riƙe da sarauta a jihar Kano

Kansilan gundumar Dayi, Dayi, Shafiu Isiaku, ya tabbatar da cewa wadanda suka jikkata na karbar magani a asibitin Dayi.

Yan bindiga sun kashe shugaban al'umma

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari da safiyar Laraba, inda suka sace shanu tsakanin hudu zuwa shida sannan suka kashe Malam Nuhu, wanda aka bayyana a matsayin fitaccen mutum kuma abin girmamawa a yankin.

Bayan labarin mutuwarsa ya bazu zuwa makwabtan kauyuka, jama'a sun fito domin farautar yan bindigar, yayin da aka ce an kama wasu da ake zargi da ba ‘yan bindigar bayanai.

Jita-jitar kisa ta kara tada hankali

An kuma yada jita-jitar cewa an kashe wani mutum ɗan asalin kauyen Gidan Maga a Abuja saboda wasu kalaman da ake zargin ya yi game da mutuwar Malam Nuhu.

Sai dai kansilan Dayi ya bayyana cewa wannan rahoto ba gaskiya ba ne.

Wani mazaunin yankin mai suna Danlami ya ce shi ma ya ji labarin, amma bai tabbatar da faruwar lamarin ba.

Gwamna Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a fadar gwamnatinsa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Matasa sun toshe hanya

Yayin da tashin hankalin ya karu, matasa daga kauyukan da ke makwabtaka suka taru a kauyen Gora, suka fara zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta tallafa wa iyalan wadanda suka mutu wajen ceto daliban Oyo

Wani mazaunin yankin, Malam Nafiu, ya ce sun toshe mahadar hanya, lamarin da ya hana motoci wucewa.

Ya ce:

"Mutane sun fito daga kauyuka daban-daban. Sun taru da yawa suka toshe mahadar hanya, babu abin hawa da ya iya wucewa."

Rahotanni sun kuma nuna cewa an kona ko lalata wasu gidaje, sai dai ba a tabbatar da girman barnar ba.

Dakarun Sojoji sun shiga tsakani

A cewar Malam Nafiu, shugaban ‘yan sandan yankin (DPO) ya yi kokarin shawo kan matasan su bude hanya, amma lamarin ya fi karfinsa, daga bisani aka tura sojoji domin karfafa tsaro a yankin.

Daga bisani Malam Nafiu ya ce an dawo da zaman lafiya, kuma an bude hanyar domin zirga-zirga ta ci gaba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Jami'an tsaro sun gwabza da yan bindiga

An ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar dakile wani harin da 'yan bindiga suka yi yunkurin kai wa a karamar hukumar Charanchi.

Jami'an tsaron sun kwato dabbobi sama da 100 da yan bindigar suka yi yunkurin awon gaba da su, inda suka fatattaki maharan bayan musayar wuta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar yan sandan Katsina ta fitar ta hannun jami’an hulda da jama’a, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262