Kwankwaso: Shawarar da Shagari Ya Taba Ba Mu tare da Janar Shehu Yar'adua

Kwankwaso: Shawarar da Shagari Ya Taba Ba Mu tare da Janar Shehu Yar'adua

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya tuna lokacin da shi da Shehu Musa Yar’adua suka ziyarci Shehu Usman Shagari
  • Mai gidansa a siyasa ya roki tsohon shugaban na Najeriya ya ba shi goyon baya kuma ya yi masa addu’ar samun sa’a
  • A ziyarar da suka kai a Sokoto, Marigayi Shagari ya fada wa Yar’adua bukatar ya zama mai hakuri da mutane a siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wata hira da ‘yan jarida kwanakin baya, a nan ya rika bayanin wasu gwal-gwalen abubuwa na tarihi da siyasa.

Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NDC, yana tare da Peter Obi a zaben 2027.

Shehu Shagari
Janar Shehu Yar'adua, Rabiu Kwankwaso da Shehu Shagari a shekarun baya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rabiu Kwankwaso ya tuna zamansu da Shehu Yar'adua

A zantawarsa da JKD Hausa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya dauko labarin farkon siyasarsa, tun lokacin yana tare da Janar Shehu Musa Yar’adua.

‘Dan siyasar ya yabi tsohon mai gidan nasa a jam’iyyar SDP, ya ce ya yi abubuwa da dama a kasa.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar gwamna a PDP bai son tazarce ya ce wa’adi 1 rak ya ishe shi

Tsohon gwamnan na Kano ya tuna lokacin da su da Marigayi Shehu Musa Yar’adua suka ziyarci tsohon shugaban Najeriya, Shehu Shagari.

Bukatar Yar'adua da suka ziyarci Shehu Shagari

Kwankwaso ya ce takanas suka ziyarci Shagari a Sokoto, bayan an gama cin abinci, an yi sallah an yi komai, sai ya nemi jin mene ne ya kawo ku.

Bude bakin Shehu Yar’adua yake da wuya, sai ya fada wa takwaransa Shehu Shagari cewa:

“Mun zo ne a kan abu uku. Na daya ayi mana addu’a. Na biyu a ba mu goyon baya. Na uku a ba mu shawara.

Sai Shehu Shagari ya ce:

“Goyon baya kuwa, Shehu ina goyon baya. Abu na biyu addu’a, Shehu Allah ba ka nasara.”

Game da abu na uku wanda shi ne neman shawara, Shagari ya fada wa tsohon sojan cewa akwai mutane sun fi 1000 da za su iya ba shi shawara.

Idan shawara yake nema, tsohon shugaban kasar ya ce Janar Yar’adua mai ritaya har sai ya ture. Tashar Premier Radio ta wallafa hirar a Facebook.

Kara karanta wannan

Mutane 4 da suka yi wa Atiku Abubakar abokan takara a tarihi daga 2007 zuwa yau

Shehu Shagari
Marigayi Shehu Shagari da ya yi mulki daga 1979 zuwa 1983 a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A na shi bangaren sai Shagari ya ba shi shawara guda cewa ya sani jarin duk wani dan siyasa shi ne jama’a, adadin magoya baya ne a gaban sa.

Shagari ya ce wajen cin zabe, adadin mutane ne a sahun gaba ba kyawun mutanen ba, yanzu dole ya rika mu’amala da mutane marasa nagarta.

Janar Shehu Yar'adua mai ritaya ya ce:

"Abin da zan ba ka shawara shi ne ka yi tsari na irin mutanen da za ka yi mu’amala da su yanzu."

Marigayin ya nuna wa Yar’adua cewa duk da ya saba da harka da manyan sojoji da sarakuna, yanzu zai hadu da mutane na kasa a cikin al’umma.

Idan kuwa zai yi hulda da jama’a irin wadannan, sai ya fada masa dole ne sai ya zama mai hakuri.

Isa Pantami sun je gidan Sule Lamido

An kawo labarin cikakken jawabin Sheikh Isa Ali Pantami a gidan Sule Lamido lokacin da aka tuna wa malamin da abubuwan da ya fada game da PDP.

Kara karanta wannan

"Ni ba ungulu ba ne:" Ganduje ya yi martani ga zargin zai hade da Kwankwaso

Isa Pantami ya fadi dalilin tashi taka-nas ta Gombe zuwa Bamaina domin ganin Sule Lamido wanda ya yi minista da gwamnan Jigawa a shekarun baya.

Sule Lamido ya tuna lokacin da Pantami yake Limamin Masallacin Jami'ar ATBU da ke Bauchi, ya sha yin wa'azi yana kiran PDP da "jam'iyyar kafirai"

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng