"Neman Gafara" Sanata Abba Moro Ya Fallasa Asallin Dalilin da Ya Sa Ƴan Siyasa ke Shiga APC
- Sanata Abba Moro mai wakiltar Bene ta Kudu ya ce ƴan siyasar da ke ficewa daga PDP zuwa APC su na haka ne don neman gafarar siyasa
- Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa ya ce dalilin da masu sauya shekar ke bayarwa ba gaskiya ba ne, akwai abin da suke ɓoyewa
- Tsohon ministan harkokin cikin gidan ya kuma yi fatali da shirin ƙulla ƙawancen ƴan adawa, yana mai cewa har yanzun PDP na nan da ƙarfinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya ce sanatoci da sauran waɗanda suka bar PDP zuwa APC masu laifi ne da ke neman mafaka.
Sanata Abba Moro ya bayyana cewa galibin ƴan siyasar da ke sauya sheka zuwa APC, suna haka ne domin neman gafara ta siyasa.

Asali: Twitter
Abba Moro, wanda ke wakiltar mazabar Benue ta Kudu, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na AIT a shirin Focus Nigeria ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A juri zuwa rafi, wata rana za mu gano dalilan da suka sa mutane ke sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyya mai mulki,” in ji shi.
Abba Moro ya yi magana kan masu shiga APC
Ya ce abu ne da aka saba da shi a siyasar Najeriya, inda ƴan siyasa ke ƙoƙarin zama cikin gwamnati domin su ci gaba da more fa’idar mulki.
"Da yawansu shugabanni ne a matakai daban-daban kama daga gwamnoni, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ‘yan majalisa.
"Don haka suna da wasu dalilai da suke ɓoye wa wanda ya sa suke komawa jam’iyyar APC.”
- Abba Moro.
Me yasa ake tururuwar shiga APC a Najeriya?
Ya kuma tuna da wata kalma da wani jigo a APC ya faɗa a baya cewa, “idan ka koma APC daga jam’iyyarka, an yafe maka laifufukanka.”
"Idan ka duba yadda wasu da ke da zunubbai da laifukan da suka aikata a baya, yanzu kuma sun koma APC, za ka fahimci cewa da gaske ne, suna neman gafara ta siyasa.”
Abba Moro ya soki wannan dabi’ar da ya ce tana barazana ga ci gaban dimokuraɗiyya da ruguza jam’iyyun siyasa.
Sanata Moro ya soki tsarin siyasar Najeriya
Sanatan ya kara da cewa:
“Shin hakan yana da amfani ga ƙasa? Ga dimokuraɗiyya? Ga ci gaban siyasar ƙasar nan? Ina manufar siyasa da ka’idojin jam’iyya?"
"Mutane suna samun nasarar zaɓe ƙarƙashin jam’iyya, amma daga bisani su canza jam’iyya da hujjar cewa sun yi hakan don maslahar mazabarsu.”

Asali: UGC
Sanata Abba Moro ya bayyana cewa PDP ba ta buƙatar haɗa kai da kowace jam’iyya kafin zaɓen 2027, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Ya ƙara da cewa duk da ficewar wasu mambobi da rashin jituwar cikin gida, PDP ta na da ƙarfi kuma za ta tsaya da kafafunta a gaba.
Da gaske Tinubu na tilastawa masu sauya sheƙa?
A wani labarin, kun ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamdele, ya ce babu wanda ke tilastawa ƴan adawa sauya sheka zuwa APC.
Sanatan na Ekiti ya musanta zargin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ke tilastawa ƴan siyasa sauya sheka.
Ya bayyana cewa sauya sheƙar da sanatocin na PDP suka yi ba wani yunƙuri ba ne na juyar da Najeriya zuwa tsarin mulkin jam'iyya ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng