Gwamna Abba Yusuf Ya Gwangwaje Hadimansa, Ya Raba Masu Manyan Filaye a Kano

Gwamna Abba Yusuf Ya Gwangwaje Hadimansa, Ya Raba Masu Manyan Filaye a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rabawa hadimansa takardun mallakar filaye domin ƙarfafa mallakar gidaje da rage matsalar ƙarancin muhalli a Kano
  • Gwamnan ya ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin iyalai, samar da dukiya da kuma gina kyakkyawar makoma ga al'umma
  • Kwamishinan filaye ya ce gwamnatin Abba ta raba filaye fiye da yadda gwamnatocin Kwankwaso da Ganduje suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rabawa wasu daga cikin hadimansa takardun mallakar filaye, yana mai cewa shirin na da nufin rage matsalar ƙarancin gidaje da kuma bunƙasa tattalin arzikin iyalai.

Waɗanda suka amfana sun haɗa da Manyan Mataimaka na Musamman (SSAs), Manyan Masu Ba da Rahoto na Musamman (SSRs), Mataimaka na Musamman (SAs), Masu Ba da Rahoto na Musamman (SRs) da Mataimaka na Kai (PAs).

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

Gwamna Abba Yusuf ya ba hadimansa kyautar filaye a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wajen wani taro. Hoto: @Kyusufabba
Source: Facebook

\Gwamna ya raba filaye ga hadimansa

A wajen rabon takardun da aka gudanar a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnatin Kano, ƙarƙashin kulawar Ma'aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane, gwamnan ya ce mallakar fili a tsarin gwamnati babbar dama ce ga masu cin gajiyar shirin in ji rahoton Channels TV.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Ibrahim, wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin bai tsaya kan rabon filaye kaɗai ba.

Ya ce:

"Wannan shiri ba rabon filaye kaɗai ba ne. Manufarsa ita ce rage matsalar ƙarancin gidaje, ƙarfafa mutane su mallaki kadarori, samar wa iyalai dukiya, da kuma ba matasa, mata da masu buƙata tushe mai ƙarfi da za su gina makomarsu."

Ya ƙara da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana cika alƙawuran da ta ɗauka, domin shugabanci na gari yana bayyana ne ta hanyar cika alƙawuran da aka yi wa jama'a.

Gwamna Abba ya yaba wa hadimansa

Kara karanta wannan

Bayan shan suka Gwamna Abba ya kare matakin ba 'yan APC filaye sama da 1500

Gwamna Yusuf ya yabawa hadiman nasa bisa goyon bayan da suka ba shi tun daga lokacin yaƙin neman zaɓe har zuwa yanzu.

Ya buƙace su da su kasance jakadun gwamnatinsa ta hanyar ci gaba da wayar da kan jama'a kan shirye-shirye da ayyukan ci gaban da gwamnatin Abba Gida-Gida ke aiwatarwa.

Kwamishina ya yi ƙarin bayani

A nasa jawabin, Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane, Abduljabar Umar, ya ce yawan filayen da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta raba ya zarce adadin da gwamnatocin tsofaffin gwamnoni Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje suka raba.

Ya kuma shawarci waɗanda suka amfana da shirin da kada su sayar da filayen, yana mai ƙarfafa su su riƙe su domin amfaninsu da na iyalansu a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com