Malamin Addini Ya Gano Kuskuren Tinubu da Zai Sa Ya Sha Kashi a Zaben 2027

Malamin Addini Ya Gano Kuskuren Tinubu da Zai Sa Ya Sha Kashi a Zaben 2027

  • Primate Elijah Ayodele ya ce wasu daga cikin mutanen da shugaban kasa Bola Tinubu ya dogara da su za su ba shi kunya a zabe mai zuwa
  • Malamin addinin ya yi ikirarin cewa an rufe wa Tinubu ido ta fuskar ruhi, yayin da wasu gwamnonin da yake dogara da su ba za su iya lashe jihohinsu ba
  • Ya kuma ce idan ‘yan adawa suka yi aiki yadda ya kamata, zai yi wa Tinubu matukar wahala ya sake lashe zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi magana kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Primate Ayodele ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana dogara da mutanen da za su ba shi kunya a zabe mai zuwa.

Ayodele ya yi magana kan tazarcen Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta ce Ayodele ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

'Ba a ji komai ba, abin da ke ciki ya fi zafi': Rarara kan wakar 'Pantami'

Malamin ya yi ikirarin cewa an rufe wa shugaban kasa ido ta fuskar ruhi, yana mai cewa wasu daga cikin gwamnonin da yake dogara da su za su ba shi kunya.

Ayodele ya yi magana kan zabe

Primate Ayodele ya ce za a yanke hukuncin zaben ne ta fuskar ruhi, yana mai zargin cewa mutane da dama da ke kewaye da Tinubu suna yaudararsa.

Ya kara da cewa dogaron da shugaban kasa yake yi da Amurka da Faransa zai iya yin tasiri mara kyau ga gwamnatinsa.

A cewarsa, babu wata kungiya ko yunkuri da zai iya tabbatar wa Tinubu nasara a zaben.

“Za a yanke hukuncin zaben ne ta fuskar ruhi saboda akwai abubuwa da dama da mutane ba sa son gani daga Tinubu kuma mutane da yawa suna yaudararsa."
“Tinubu ba shi da cikakken iko kan gwamnatinsa a yanzu, sai idan ya samu mutanen da za a iya dogara da su, amma ban ga irin wadannan mutane tare da shi ba."

Kara karanta wannan

Yadda malaman addinin Kirista suka kai ruwa rana da Tinubu a Aso Villa

“Har yanzu yana dogara da gwamnonin da za su ba shi kunya saboda ba dukkansu ne za su lashe jihohinsu ba."
“Baya ga haka, dogaron da Tinubu yake yi da Amurka da Faransa domin samun nasara zai kara shafar sa, amma an rufe masa ido ta fuskar ruhi."
“Ba a hannun wata kungiya ko kudin da suke rabawa yake ba, amma bai shirya ya saurara ba.”

- Primate Elijah Ayodele

Gargadi kan ‘yan adawa

Ayodele ya ce idan ‘yan adawa suka bi hanyar da ta dace, zai yi wa Tinubu matukar wahala ya sake lashe zabe.

Ya kuma yi ikirarin cewa ko Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba za ta iya tabbatar masa da nasara ba.

“Sai idan ‘yan adawa ba su yi aiki yadda ya kamata ba ne shugaban kasa zai sake lashe zabe, in ba haka ba, zai yi matukar wahala."
“Abin da suke yi shi ne kokarin kyautata hoton shugaban kasa, amma ko INEC ba za ta iya ba shi nasara ba.”

- Primate Elijah Ayodele

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi yanayin da zai sa ya shiga daji ceto daliban da aka sace

Primate Ayodele ya hango matsala ga Tinubu
Primate Elijah Ayodele na jawabi a coci Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele
Source: Facebook

Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare 'yancin addini a kasar.

Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya ce zai yi hakan ne kamar yadda kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng