Bincike Ya Shiga Matatun Mai, EFCC Ta Kai Tsohon Shugaban Matatar Fatakwal Kotu

Bincike Ya Shiga Matatun Mai, EFCC Ta Kai Tsohon Shugaban Matatar Fatakwal Kotu

  • Hukumar EFCC ta fara shari’a da Ahmed Dikko wanda kwanaki ya sauka daga shugabancin kamfanin PHRC
  • Lauyan gwamnati, Ekele Iheanacho SAN ya zargi tsohon shugaban PHRC da hannu a badakalar fiye da N1.3bn
  • Ikechukwu Ajunwa SAN ya wanke wanda ake tuhuma daga zargi kuma ya yi nasarar samun belin shi a kotun tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A ranar Laraba, 7 ga watan Yuli 2026, hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Darektan kamfanin PHRC da ke Fatakwal a kotu.

EFCC ta yi karar Ahmed Dikko bisa zargin wanke kudin haramun a lokacin da yake shugabantar babbar matatar mai a Fatakwal, jhar Rivers.

Matatar mai
Matatar mai da ke Fatakwal, jihar Rivers Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukumar EFCC ta yi karar tsohon shugaban PHRC

Bayanai daga shafin EFCC a X ya nuna an gurfanar da Ahmed Dikko a kotun tarayya a Abuja tare da kamfanin Masterpiece Projects & Investment Limited.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ba ICPC umarni kan ma'aikatar bogi

Dikko ya bayyana gaban Alkali Inyang Ekwo bisa zargin aikata wasu laifuffuka 12 da suka shafi wanke kudin haram a sa’ilin da yake rike da PHRC.

An bada belin Ahmad Dikko a kotu

Da lauyoyin hukumar EFCC suka karanta jerin zargi 12 da ake yi masa, tsohon darektan ya ce bai aikata su ba kuma saboda haka ne aka bada belin shi.

Ikechukwu Ajunwa SAN ya yi kokarin ganin an bada belin wanda ake tuhuma duk da adawar Ekele Iheanacho SAN a madadin gwamnatin tarayya.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bada belin Dikko a kan N150m tare da kawo wanda zai tsaya masa.

Bayan haka, alkali ya tsaida ranakun 12, 13 da 14 na watan Oktoban 2026 a matsayin lokacin da za a fara sauraron karar da EFCC ta shigar.

Zargin da EFCC ta ke yi wa Dikko

Lauyan EFCC, Ekele Iheanacho SAN ya zargi Dikko da mallakar wani gida a Abuja daga cikin kudin da ya ce ya samu ta haramtacciyar hanya.

Kamar yadda aka ji daga Business Day, an kai karar ne a sanadiyyar binciken da ake yi game da N1.32bn da aka karkatar da sunan gyaran matatun mai.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya hukunci a shari'ar da hukumar EFCC ta nemi ƙwace kadarorin Malami

Daga cikin zargin akwai biyan kudi N218m ga wani Hadejia Bashir domin mallakar gida a unguwar Katampe Extension a birnin tarayya Abuja.

An kuma zargi Dikko da samun N100m ta asusun bankinsa. Ana zargin kamfanin Ebenco Global Link Limited ya tura kudin a dalilin wata kwangila.

Akwai zargi masu yawa da suka shafi samun kudi daga wajen ‘yan kwangila. Lauyan wanda ake kara, Ikechukwu Ajunwa ya karyata duka zargin.

Rigimar jami'an ICPC da Nasir El-Rufai

ICPC ta hana Nasir El-Rufai zuwa asibiti, ta kama likitansa, ta doki matarsa. ADC ta yi wannan zargi kamar yadda aka samu rahoto a makon nan.

Kakakin ADC ya ce sai da aka make wata matar Nasir El-Rufai bayan ICPC ta kama likitansa kuma an hana shi zuwa asibiti duk da alkali ya amince.

Bolaji Abdullahi ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kama-karya, kuma a madadin jam'iyyar hamayyar suka bukaci a sake duba batun belin shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng