Yadda 'Yan Bindiga Suka Samu Miliyoyi bayan Sace Babban Alkali a Najeriya
- Iyalan Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruk Hassan Bunza, sun tabbatar da cewa sun biya Naira miliyan 50 domin ceto shi daga hannun masu garkuwa da mutane
- Iyalan sun ce masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 200, amma daga bisani suka amince da karɓar Naira miliyan 50 bayan shafe kwanaki ana tattaunawa
- Rundunar 'yan sandan Kebbi ta tabbatar da sakin alƙalin, tana mai cewa jami'an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen farautar waɗanda suka sace shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Birnin Kebbi – Iyalan Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruk Hassan Bunza, sun tabbatar da cewa sun biya Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa domin a sako shi daga hannun masu garkuwa da mutane.
An sace Mai Shari'a Bunza ne a safiyar ranar 26 ga Yulin 2026, lokacin da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai hari gidansa da ke ƙaramar hukumar Bunza a jihar Kebbi.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa alƙalin ya samu 'yanci ne a ranar Litinin bayan ya shafe kwanaki takwas a hannun masu garkuwa da shi.
Yadda aka biya kuɗin fansa
Wani ɗan uwan Mai Shari'a Bunza, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 200 kafin daga bisani su rage zuwa Naira miliyan 50.
Ya ce har yanzu alƙalin yana samun kulawa a gidansa domin murmurewa daga halin da ya shiga yayin zaman garkuwa.
A cewarsa:
"Har yanzu muna kula da shi a gida tun bayan da aka sake shi ranar Litinin. Yana buƙatar lokaci domin murmurewa daga tashin hankalin da ya fuskanta."
Ya ƙara da cewa iyalan za su yi wa manema labarai ƙarin bayani kan abin da ya faru bayan alƙalin ya samu cikakkiyar lafiya.
Abin da masu garkuwar suka nema
Wani ɗan uwan alƙalin ya shaida cewa kafin a kai kuɗin fansar, masu garkuwar sun umarci iyalan su kawo kwalaben maltina guda biyar da kuma kwalaben Dudu guda biyar.
Leadership ta rahoto ya ce sun buɗe abubuwan shan a gabansu, suka sha kafin daga bisani su karɓi kuɗin fansar.
Iyalan sun kuma bayyana cewa an dawo da Mai Shari'a Bunza gida tsakanin ƙarfe 6:00 zuwa 7:00 na safiyar Litinin, inda aka sauke shi daga motar da ke ɗauke da itace.
'Yan sanda sun yi martani
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da sakin Mai Shari'a Bunza tare da bayyana cewa ya koma gida lafiya.
Sai dai rundunar ta ce duk da cewa masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa, ta tsaya kan matsayarta na rashin amincewa da biyan kuɗin fansa.

Source: Twitter
Ta kuma ce jami'an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da bincike domin gano masu laifin tare da gurfanar da su a gaban shari'a.
Maganar Obi kan sace mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce da ace shi ne shugaban ƙasa, da kansa zai shiga daji domin jagorantar aikin ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Oriire da ke jihar Oyo.
Obi ya ce ba zai jira sama da kwanaki 50 kafin ɗaukar mataki ba, yana mai cewa dole ne gwamnati ta nuna ƙwazo wajen ceto duk waɗanda ke hannun masu garkuwa.
Ya kuma soki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin rashin tuntuɓar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a lokacin da aka sace ɗaliban.
Asali: Legit.ng


