Sanata Hanga Ya Yi Magana bayan Kwankwaso Ya Tankwabe Takararsa, An ba wa Gawuna

Sanata Hanga Ya Yi Magana bayan Kwankwaso Ya Tankwabe Takararsa, An ba wa Gawuna

  • Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, ya yi magana bayan an ba Dr. Nasiru Yusuf Gawuna tikitin takarar Sanata na 2027
  • Sanata Hanga ya ce an yi masa adalci kuma an cimma matsaya kan zaɓin Gawuna bayan tattaunawa domin Kwankwasiyya ta ci gaba
  • Ya jaddada biyayyarsa ga jagoran Kwankwasiyya, tare da bayyana cewa soyayyasa ga akidar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa'i Sani Hanga ya yi magana a karon farko bayan an sauya tsarin takararsa ta 2027, inda aka miƙa tikitin ga tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

A makon da ya gabata ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da Gawuna, wanda tun farko ake sa ran za a ba shi tikitin takarar gwamna a jam'iyyar NDC, a matsayin wanda zai yi takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Gawuna da Gwarzo: Kwankwaso ya fitar da dan takarar gwamnan Kano na 2027

Sanata Rufa'i Hanga ya yi biyayya ga Kwankwaso
Sanat Rufa'i Hanga tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

A wata hira da aka wallafa a shafin Facebook na Express Radio, Sanata Hanga, wanda ke riƙe da kujerar a halin yanzu, ya bayyana cewa an yi adalci a tsarin da tafiyar Kwankwasiyya ta bi wajen yanke hukuncin.

Rufa’i Hanga ya yi magana a kan Gawuna

Sanata Rufa'i Hanga ya bayyana cewa ba haka kawai aka miƙa wa Gawuna tikitin takara ba, yana mai cewa an yi zama tare tare da tattaunawa kafin a cimma matsaya kan zaɓin.

Ya ce yana da tabbacin cewa an yi masa adalci, kuma bai damu da ba wa Gawuna tikitin takarar ba saboda an fahimci cewa zai kasance mai amfani ga tafiyar Kwankwasiyya.

Hanga ya ce da yawunsa aka mika takarar kujerar da ya ke kai ga Gawuna
Nasiru Yusuf Gawuna a taron koma wa ADC a jihar Kano Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Twitter

A cewar Sanata Hanga:

"Mu a wannan tafiya tamu ta Kwankwasiyya, iyali ne mu baki ɗaya. Yaya za a yi tsarin da za mu yi nasara? Yaya za a yi tsarin da kowa zai ji an tafi da shi? Wannan shi ne tsarinmu."

Kara karanta wannan

"Ko Ganduje ba zai ce shi ba yarona ba ne": Kwankwaso ya yi martani ga Abba

"Kuma mun san ƙarfinsa da jama'arsa, kuma mun san ƙarfinsa da jama'arsa."

Ya ƙara da cewa wannan na daga cikin dalilan da suka sa aka ba Gawuna takarar domin a yi tafiya tare kuma a cimma nasara tare.

Hanga ya jaddada mubaya’a ga Kwankwaso

Sanata Rufa'i Hanga ya bayyana cewa adalci da ƙoƙarin da Kwankwaso ke yi domin tabbatar da cewa talakawa sun samu mafita ne suka sa ya haɗa tafiyar siyasarsa da jagoran Kwankwasiyyar.

A cewarsa:

"Na san waye shi, na san adalcinsa, na san zuciyarsa. Harka ce yake yi saboda talakawa."

Hanga ya ce tun da ya fara mu'amala da Kwankwaso ya fahimci cewa manufarsa ita ce inganta rayuwar marasa ƙarfi da talakawan al'umma.

Ya nanata cewa Kwankwaso mutum ne mai tausayi ga talakawa da masu ƙaramin ƙarfi a cikin al'umma, kuma babban burinsa shi ne ya samu damar taimaka wa jagoran Kwankwasiyya wajen cimma manufofin tafiyar siyasar.

Kwankwaso ya ba Abdussalam takara a Kano

A baya, mun kawo labarin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa a ranar Juma'a, 29 ga Mayun 2026 za su kaddamar da 'yan takarar da za su wakilci NDC a 2027.

Kara karanta wannan

NDC: An gano wanda Kwankwaso ke so ya tsayar ya fafata da Abba a Kano

Sanata Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa NDC takarar gwamnan Kano idan Allah Ya kai mu lokacin zaben.

Ya kuma bayyana jin dadi game da mika takarar Sanatan Kano ta Tsakiya ga tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da aka rika zaton shi ne zai samu takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng