An Gano Bayanai kan Ƙirƙirar Hukumar PFIPC bayan an Kammala Binciken ICPC
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta ICPC mai zaman kanta ta ce ta kammala binciken da aka yi kan PFIPC, ana jiran mika rahoto.
- Kwamitin Majalisar Wakilai ya yi magana game da sakamakon binciken, tare da bayyana lokacin da za a saki cikakkun bayanan da aka gano
- Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargin ya yi karifn hali a kan PFIPC ya nace ba shi kaɗai ya ƙirƙiri hukumar ba, yana neman a ba shi damar kare kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta kammala binciken da ta gudanar kan takaddamar da ta shafi hukumar bogi ta PFIPC, wadda ta jawo cece-kuce a Najeriya.
Rahotanni sun ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ICPC wa'adin kwanaki 30 tun ranar 7 ga Yulin 2026 domin ta binciki lamarin tare da gabatar da rahoto.

Source: Facebook
Majiyoyi daga cikin ICPC sun shaida wa Daily Trust cewa an riga an yi wa babban wanda ake zargi, Prince Adeniyi Adeyemi, tambayoyi yayin da yake tsare.
An yi binciken hukumar PFIPC
Trust Radio ta ruwaito cewa majiya ta shaida wa jaridar cewa an yi masa tambayoyin ne a makon da ya gabata inda aka yi masa tambayoyin a gaban lauyansa.
Majiyar ta ce:
"An riga an yi wa wasu mutane tambayoyi kafin wannan. Ina ganin yanzu ana kammala rahoton ne kuma za a gabatar da shi kafin wa'adin ya cika."
A gefe guda kuma, kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken lamarin ya ce zai sanar da 'yan Najeriya abin da ya gano cikin wannan makon kafin ya mika cikakken rahotonsa ga majalisar.
Bayanai kan PFIPC za su bayyana
Shugaban kwamitin, Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana cewa binciken ya gano abin da ya kira babbar damfara, ciki har da ƙirƙirar wani sashen gudanarwa da aka danganta da Fadar Shugaban Ƙasa, wanda bincike ya nuna babu shi a zahiri.
Ya ce kwamitin bai samu damar sauraron Adeyemi kai tsaye ba saboda yana tsare bisa umarnin kotu, amma ya tabbatar da cewa za a ba dukkan ɓangarorin damar a ji su kafin a kammala binciken.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Festus Akhigbe ta fitar, sun buƙaci kwamitin ya ba shi damar bayyana a gabansa.
Sanarwar ta ce:
"Duk wani sakamakon bincike ko rahoton majalisa da aka fitar ba tare da an ba wa wanda muke karewa damar kare kansa ba, zai kasance mai manyan kura-kurai, bai cika ba kuma ya saɓa wa haƙƙinsa na samun adalci."
Adeyemi ya yi fallasa kan PFIPC
A baya, mun kawo labarin cewa Adeniyi Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun amince ko sun yi hulɗa da hukumar da ake takaddama a kanta tun bayan da aka gani ta bogi ce.
Lauyoyinsa sun buƙaci a ba shi damar bayyana gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke bincike kan badakalar PFIPC domin a ba shi cikakkiyar damar kare kansa daga zarge-zargen.
Sun ce fitar da rahoto ba tare da sauraron Adeyemi ba zai saɓa wa haƙƙinsa na samun adalci a binciken da ake yi bayan an fito da sunansa a duniya da zargin badakalar kafa hukuma guda.
Asali: Legit.ng

