Bidiyon Dan Takarar Gwamnan ADC Yana Raba Dafaffiyar Masara Ya Dauki Hankalin Jama'a
- Dan takarar gwamnan ADC a Oyo, Taofeek Adegoke ya tayar da kura a kafofin sadarwa yayin taron siyasa wanda al'umma suka cika
- Lamarin ya ja hankali ne bayan bidiyonsa yana rabon dafaffiyar masara ga magoya baya ya bazu a kafafen sada zumunta
- Magoya bayansa sun yi ta kiransa "Gwamna", suna karbar masarar kai tsaye daga hannunsa, yayin da wasu suka ce hakan alama ce ta tawali'u
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a Oyo, Taofeek Adegoke, ya tayar da kura a ranar Talata bayan wani bidiyonsa.
An gano bidiyon inda ya nuna yana rabon dafaffiyar masara ga magoya bayansa a bakin hanya ya yadu sosai.

Source: Instagram
A cikin bidiyon da ya yadu, an ga Adegoke tsaye kusa da tukunya cike da dafaffiyar masara yana mikawa magoya bayansa da suka taru domin karba, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a
Magoya bayan sun yi ta kokarin karbar masarar kai tsaye daga hannunsa, suna kiransa da lakabin "Gwamna" tare da rera taken goyon bayansa cikin farin ciki.
Wasu daga cikinsu sun dage cewa sai sun karbi masarar daga hannun Adegoke da kansa, suna bayyana wannan a matsayin wata albarka yayin da suke mikar da hannayensu cikin taron jama'a.
Tun daga lokacin, bidiyon ya jawo martani da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu magoya baya suka yaba wa dan takarar ADC saboda abin da suka kira tawali'unsa da kuma kusancinsa da talakawa.
Sai dai wasu sun ce irin wadannan abubuwa sun zama ruwan dare a lokacin yakin neman zabe, lokacin da 'yan siyasa ke kokarin nuna cewa suna tare da jama'a.
Nuna irin wannan tawali'u a bainar jama'a ya zama wani bangare na yakin neman zabe a Najeriya.
A lokutan neman kuri'u, ana ganin 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban suna cin abinci a wuraren sayar da abinci na kan hanya, ziyartar kasuwanni, hawa babur da adaidaita sahu, da halartar tarukan al'umma domin kara kusantar masu kada kuri'a.
Yayin da magoya baya ke kallon irin wadannan matakai a matsayin hujjar saukin kai da tausayin jama'a, masu suka suna ganin dabarun neman kuri'u ne kawai domin jan hankalin masu zabe.
Da yake martani ga bidiyon, wani mai amfani da TikTok mai suna Sam Oladayo ya ce:
"Gwamna mai tawali'u sosai, mu hada kai mu mayar da shi Shugaban Kasar Amurka."
Wani mai suna Finiyi Samuel ya ce:
"Mutanen da ke binsa sun san ba zai lashe zaben ba, amma duk da haka za su bi shi su karbi kudinsa."
Shi kuwa Ayinla Kusela ya rubuta:
"Karya ce kawai. Wannan tsohuwar dabarar yaudarar jama'a ce."
Atom ya ce:
"Tsohuwar hanyar yaudarar mutane."
A nasa bangaren, Afolayan Femi ya ce:
"Baya ga tsayawa takarar gwamna, mutum ne nagari."
Gwamna Makinde ya caccaki Bola Tinubu
An ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce cire tallafin man fetur da barin darajar naira ta riƙa sauyawa lokaci guda sun ƙara tsananta rayuwa ga ‘yan Najeriya.
Makinde ya ce babu ƙasar da za ta iya jure irin waɗannan manyan sauye-sauyen tattalin arziki biyu a lokaci guda ba tare da matakan rage radadin tasirinsu ba.
Jam’iyyar APM ta ce za ta haɗa kai da jama’a domin kawo sauyi a Najeriya tare da ƙarfafa tattalin arziki da tsaro a 2027.
Asali: Legit.ng
