2027: 'Dan Shugaba Tinubu Ya Jawo Gagarumar Matsala kan Abin da Ya Yi Wa Matasan Arewa

2027: 'Dan Shugaba Tinubu Ya Jawo Gagarumar Matsala kan Abin da Ya Yi Wa Matasan Arewa

  • Wata kungiyar matasan Arewa ta yi barazanar janye goyon bayan Shugaba Bola Shmed Tinubu a zaben 2027 kan abin da ɗansa ya yi
  • Kungiyar ta zargi Seyi Tinubu da fifita matasan Yarabawa wajen nade-nade da shugabancin kungiyoyin matasa
  • Ta ce shugabannin kungiyoyin goyon bayan APC 1,378 a Arewa za su fara tuntuba da nazari kan matakin da za su dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wata sabuwar takaddama ta siyasa na kara kunno kai a cikin jam'iyyar APC, bayan wani taron shugabannin kungiyar matasan Arewa ta North-West APC Youth Stakeholders' Forum.

Rahoto ya nuna cewa taron ya gudana karkashin jagorancin Hon. Bashir Ruma da kuma shugabannin kungiyar Arewa Democratic Youth Stakeholders' Forum.

Seyi Tinubu.
Seyi Tinubu, dan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da wakilan matasa Hoto: Seyi Tinubu
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya nuna cewa kungiyar ta yi zargin cewa ana ci gaba da ware matasan Arewa daga manyan mukaman shugabancin matasa da kuma yanke shawara a cikin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, babban jigo ya tayar da rigima a APC kan takarar shugaban ƙasa a 2027

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Amb. Salawudeen Shaibu, ya sanya wa hannu,

Kungiyoyin APC a Arewa za su hada kai

Kungiyar ta bayyana cewa za ta hada kan shugabannin kungiyoyin goyon bayan APC a fadin Arewa domin kalubalantar abin da ta kira siyasar bangaranci da rashin adalci.

Ta kuma sanar da nada Hon. Haruna Sardauna da Mallam Idiriss Jibrin a matsayin masu kula da yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya domin jagorantar tuntuba da masu ruwa da tsaki.

Kungiyar matasan ta ce ta umarci shugabannin kungiyoyin goyon bayan APC 1,378 da ke jihohin Arewa 19, da Sbuja su fara tuntuba kan yiwuwar janye goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Seyi Tinubu ya fusata matasan Arewa

Kungiyar ta yi zargin cewa Seyi Tinubu, dan Shugaba Bola Tinubu, na taka rawa wajen tsara shugabancin matasa da nade-naden da suka shafi matasa ta hanyar da ke fifita matasan yankin Yarabawa.

Kara karanta wannan

Yan Arewa sun taso Kiristoci a gaba kan Tinubu, sun sha alwashi kan zaben 2027

Ta kuma yi ikirarin cewa mukaman da suka shafi matasa a gwamnati da jam'iyya sun fi karkata ga mutane daga yankin Kudu maso Yamma, lamarin da ta ce ya haifar da jin an ware matasan Arewa.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Ana zargin nunawa yan Arewa wariya

Kungiyar ta kuma yi zargin cewa ana bai wa wasu kungiyoyin matasa daga yankin Yarabawa kulawa da tallafi fiye da kungiyoyin da matasan Arewa ke jagoranta.

Ta kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da cewa nade-nade da damar siyasa suna nuna adalci da wakilcin dukkan yankunan Najeriya, cewar rahoton Guardian.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Fadar Shugaban Kasa, shugabannin APC na kasa da kuma Seyi Tinubu ba su fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen da kungiyar ta yi ba.

Jigo ya maka APC a kotun tarayya

A wani rahoton, kun ji cewa wani babban jigon APC, Alhaji Bayero Lawal, ya tayar da rigima ta hanyar maka jam’iyyarsa a kotu kan batun takarar shugaban kasa a 2027.

Bayero Lawal ya kai kara kotu ne bisa zargin APC da hana shi sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takarar shugaban kasa.

Ya bayyana cewa shi cikakken mamba ne na APC wanda ke biyan dukkan hakkokin jam’iyya, don haka kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ba shi cikakken 'yancin neman kowace kujera ta zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262