Babu Sunan Jonathan a ‘Yan Takaran PDP, Wike Ya Samu Yadda Yake So wajen INEC
- Tsagi a cikin jam'iyyar PDP da ke tare da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tura sunayen ‘yan takara a shafin INEC
- A zaben shugaban kasa, Sandy Onor, tare da abokin takararsa Babangida Umaru za su rike wa PDP tuta a shekara mai zuwa
- Shugaban tsagin, Abdulrahman Mohammed, ya bayyana wannan a matsayin cika alkawarin da suka yi wa 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Tsagin jam’iyyar PDP da ke da goyon bayan Nyesom Wike, ya daura sunayen ‘yan takara na zaben da za a yi a shekarar 2027.
Bangaren Ministan Abuja sun bayyana cewa ‘yan tsaginsu ne suka samu shiga shafin INEC, kenan suke da halatattun masu yin takara.

Source: Getty Images
Jam'iyyar PDP ta daura 'yan takara a shafin INEC
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa na tsagin Nyesom Wike, Abdulrahman Mohammed ya shaida haka ranar Lahadi a cewar Premium Times.
Abdulrahman Mohammed ya sanar da magoya baya da sauran ‘yan kasa cewa sun yi nasarar daura sunayen ‘yan takararsu a shafin INEC.
Hakan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan Nyesom Wike ya yi magana, inda ya nuna cewa jam’iyyarsu ba za ta iya lashe zaben 2027 ba.
Sanarwar da Abdulrahman Mohammed ya fitar ta bayyana cewa sun daura sunan ‘yan takarar zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya.
Abdulrahman Mohammed ya ce:
“Ina mai farin cikin sanar da dukkanin ‘yan PDP da ‘yan Najeriya cewa babbar jam’iyyarmu, a karkashin jagoranci na, ta daura sunayen ‘dan takarar shugaban kasa da abokin gaminsa da kuma na ‘yan takarar majalisar tarayya a shafin INEC.”
Ina makomar takarar Goodluck Jonathan a PDP?
Kowa ya san cewa Nyesom Wike wanda minista ne a karkashin gwamnatin APC, yana goyon bayan tazarcen Bola Tinubu ne a 2027.
Da wannan nasara da aka samu a kan bangaren Kabiru Tanimu Turaki, akwai yiwuwar babu zancen takarar Goodluck Jonathan a jam'iyyar adawar.
A wajen Kabiru Tanimu Turaki SAN, ‘dan takarar PDP a zaben shugaban kasa shi ne Dr. Jonathan duk da bai taba cewa ya shiga zaben ba.

Kara karanta wannan
Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027
Tsagin Wike kuwa ya tsaida tsohon sanata. Sandy Onor da Babangida Umaru a zaben na shugaban kasa.

Source: Getty Images
PDP za ta daura 'yan takara na jihohi
The Cable ta ce Mohammed ya ce daura sunayen ‘yan takarar ya tabbatar masu da cewa su za su shiga kamar yadda suka yi alkawari.
Ya ce yanzu abin da ya rage shi ne su daura sunayen ‘yan takarar gwamna da na masu neman zuwa majalisar dokoki a shafin hukumar.
“Yayin da mu ke jiran daura sunayen ‘yan takararmu na gwamna da majalisar dokoki, a madadin majalisar gudanarwa na jam’iyyarmu, ina taya daukacin ‘yan PDP a fadin Najeriya da duniya murna.”
- Abdulrahman Mohammed
Nan gaba kadan za a tabbatar da wadanda za su yi wa PDP takara a zaben gwamna tsakanin tsagin Tanimu Turaki da Nyesom Wike.
Legit Hausa ta fahimci daga cikin inda ake sauraron makomar PDP akwai Gombe inda Farfesa Isa Pantami yake son zama gwamna.
Takarar Pantami na ta karfi a PDP
Ana da labari cewa wani malamin jami’a yana ganin Isa Ali Pantami zai iya zama gwamna a karkashin jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Kabir Danladi Lawanti PhD ya jero malanta da wasu abubuwa da suka budewa Isa Ali Pantami hanya a takarar gwamnan Gombe a PDP.
Dr. Kabiru Lawanti yake cewa malamin yana samun karbuwa ne saboda batun addini kuma APC ta gagara shawo kan matsalar 'yan takara.
Asali: Legit.ng

