Tsohon Dan Majalisar da Ya Yafe Takara Ya Koma Kasuwa Ya Dawo Zai Yaki Tinubu
- Hon. Abubakar Cika Adamu ya wakilci Shiroro/Rafi/Munya a Majalisar tarayya kafin ya hakura da kujerar tun a shekarar 2019
- Tsohon ‘dan majalisar ya rubuta takarda zuwa ga APC ya ce ba zai sake takara ba, ya zabi ya koma harkokin kasuwanci
- Ganin halin da al’umma suke ciki a yau, ya dawo fagen siyasa amma ba da nufin ya tsaya takarar wata kujera a zabe shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Abubakar Cika Adamu tsohon ‘dan majalisar tarayya ne, amma a yau yana nadamar kujerar da ya rike a baya.
Hon. Abubakar Cika Adamu ya wakilci mazabar Shiroro/Rafi/Munya a majalisar wakilan tarayya daga 2015 zuwa 2019.

Source: UGC
Abubakar Cika Adamu ya yi nadamar zuwa majalisa
A wata hira da aka yi da shi kwanaki a tashar DC Hausa, ‘dan siyasar ya koka da rashin adalci wajen rabon albarkatun kasa.
Abubakar Cika Adamu ya koka da cewa a zaman da ya yi a majalisa, bai iya kawo wa mutanen mazabarsa wani abin a yaba ba.
A tsarin da ake tafiya a kai, tsohon ‘dan siyasar ya ce da wahala talakawa su amfana sai dai idan mutum zai shiga a yi zalunci da shi.
Tsohon ‘dan majalisar wanda ya ci zabe a jihar Neja a karkashin APC ya nuna yadda matsalar rashin tsaro ya kara tabarbarewa a kasar.
Baya ga matsalar tsaro, ‘dan siyasar ya yi tir ganin yadda gwamnati ta gaza inganta harkokin ilmi da wutar lantarki a mulkin farar hula.
An taba ganin bidiyonsa shafin majalisa a Facebook, yana cewa dole ne a kawo sauyi wajen yadda ake tafiyar da Najeriya gaba daya.
Hon. Abubakar Cika ya yafe takara a 2019
Daga karshe dai, Daily Post ta rahoto cewa ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC takarda, ya ce ba zai sake neman yin takara ba.
“Ka ga na yi Majalisar tarayya, a yau na yi nadama da na yi Majalisar tarayya, haka Allah ya kaddaro mani, amma ga ba na fata,
"Shiyasa ka ga na rubuta takarda da kai na, na ce ba zan kara takara ba saboda ban ga amfanin zama na a majalisa ko amfanin yin majalisa ba.”
Tsohon 'dan majalisa ya ce akwai lalata a harkar
A hirar da YMB Hausa ta dauko kuma ta daura a Facebook, Hon. Cika Adamu ya ce dama yana siyasa ne saboda harkar ta zama dole.
A cewarsa ta siyasa ne kurum za a iya canza shugaba, amma dai shi ba zai tsaya takara ba domin ya san lalata ne a cikin tsarin.
Ko da ya je majalisa a 2015, ya ce mutanen garinsu suka saya masa fam. Shi Hon. Cika yana ganin hauka ne mutum ya nemi mulki.
Hon. Abubakar Cika zai yaki tazarcen Bola Tinubu
Yanzu ya dawo ana damawa da shi a siyasa saboda a cewarsa Bola Tinubu ya gallaza wa jama’a don haka dole a yake shi kafin 2027.
Muddin Tinubu ya zarce, tsohon ‘dan jam’iyyar na APC da ke mulki yana ganin tamkar an kai mutane mayanka ne za a datse kawunansu.
A hirar da aka yi da shi, ya roki Allah SWT ya kawo wa jama'ar Najeriya mafita a duk tsarin da ya dace.

Source: Getty Images
Shaidar da aka yi wa tsohon 'dan majalisar
Da ya gama takara a 2019, an ji ya koma kasuwa, kuma da alama dai ya samu shaida mai kyau daga wadanda mu’amalar kudi ta hadu su.
Wani mai suna Ibrahim El-Caleel ya bayyana cewa ya san wannan bawan Allah kuma ya yi mamaki sosai da ya ji labarin tsohon ‘dan majalisa ne.
Injiniya El-Caleel ya yabi ‘dan siyasar da kasancewa mai amana, maras yaudara kuma yana gudun karbar bashi sannan ga tsaida sallah.
“Haƙiƙa wannan mutumin kirki ne a babin mu’amala. Na san shi; customer ɗina ne. Kana iya amince masa akan harkar kuɗi. Ba ya yaudara. Duk da irin yadda kasuwanci ya zama yanzu, ana dogara da bashi, shi wannan mutumin na sha gwada bashi credit facility amma yana ƙin karɓa. Sannan ba ya wasa da sallah; kai, ladanin masallaci ne ma!
“Ranar da aka fara faɗa mini cewa Former Member ne na House of Representatives, na yi mamaki ƙwarai. Domin kuwa mutum ne har mutum. Bai yi kama da ƴan siyasan Najeriya ba kwata-kwata.”
- Ibrahim El-Caleel
A karshe ya Ibrahim El-Caleel rubuta a shafin nasa na Facebook:
“Abinda ya bayyana gare ni kenan. Allah ne Ya san shi iyakar sani.
Ina masa fatan alheri. Allah Ya ƙara masa istiƙamah. Ameen. Ameen.”
Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirorin majalisa
Labari ya zo cewa ‘yan majalisa sun yi kudiri sun turo Aso Rock, amma Shugaba Bola Tinubu ya jefa shi a bola saboda bai gamsu da wasu abubuwa a ciki ba.
Bola Tinubu ya ki sanya hannu kan wasu kudurori biyu da Majalisar Tarayya ta amince da su, ya fada masu bai gamsu da gyaran fuskar da sanatocin suka yi ba.
A tashin farko shugaban kasar ya bayyana cewa akwai kura-kurai da nakasu a cikin ƙudirin da ke neman yi wa dokar hukumar RMRDC kwaskwarima a Najeriya.
Asali: Legit.ng



