Shin da Gaske ne Cewa Sarkin Musulmi Ya Ce a Zabi Tinubu a 2027?

Shin da Gaske ne Cewa Sarkin Musulmi Ya Ce a Zabi Tinubu a 2027?

  • Wani bincike ya nuna cewa Sarkin Musulmi bai bayyana Bola Tinubu a matsayin zaɓin Fulani kaɗai a zaɓen 2027 ba kamar yadda aka yaɗa a kafafen sada zumunta
  • An gano cewa bidiyon da ake yaɗawa ya fito ne daga taron ƙungiyar MACBAN, inda Sultan ya yabawa gwamnatin Tinubu kan kafa Ma'aikatar Bunƙasa Kiwo
  • Binciken ya tabbatar da cewa Sultan bai yi kira ga 'yan Najeriya su zaɓi Tinubu karo na biyu ba, kuma babu inda ya nemi a kafa hukumar Fulani ko ma'aikata ta musamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani bincike da aka gudanar ya karyata ikirarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zaɓin Fulani a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi ga yan Najeriya game da addininsu

An kuma gano cewa Sultan bai yi kira ga gwamnatin tarayya ta kafa wata hukumar Fulani ko ma'aikata ta musamman domin magance matsalar ta'addanci ba kamar yadda wasu suka yi ikirari.

Bola Tinubu da Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi na gaisawa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dubawa ta rahoto cewa binciken ya biyo bayan wani saƙo da wani mai amfani da shafin X ya wallafa a ranar 1 ga Agustan 2026.

Abin da Sultan ya faɗa a zahiri

Binciken ya gano cewa bidiyon da ake yaɗawa ya fito ne daga bikin buɗe taron ƙasa na shekarar 2026 na ƙungiyar Miyetti Allah ta MACBAN da aka gudanar a Abuja.

Bayan nazarin cikakken jawabin Sultan, an tabbatar da cewa bai yi magana kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ko neman a sake zaɓen Tinubu ba.

Maimakon haka, ya yabawa shugaban ƙasa bisa kafa Ma'aikatar Bunƙasa Kiwo, yana mai cewa matakin ba a taɓa ɗaukarsa ba a tarihin ƙasar.

A cikin jawabin nasa ya ce:

"Ko kuna so ko ba ku so, gaskiya wannan abu ne da ba a taɓa yi ba. Dole mu gode masa, mu ƙara ba shi goyon baya domin ya ci gaba da ayyukan alherin da yake yi wa wannan ƙasa."

Kara karanta wannan

Gwamna ya ji zazzafan martani da ya tabo Kwankwaso, Obi a Kudancin Najeriya

Ya kuma gode wa shugaban ƙasa kan kafa kwamitin sake fasalin harkokin kiwo, yana mai bayyana fatan cewa matakan za su amfani makiyaya da manoma.

Bincike ya karyata zargin

Binciken ya nuna babu wani wuri da Sultan ya ce "Tinubu ne zaɓinmu kaɗai" ko ya buƙaci 'yan Najeriya su zaɓe shi a wa'adi na biyu.

Haka kuma, rahotannin daga kafafen da suka wallafa game da taron ba su ambaci wani goyon bayan siyasa ga Tinubu ba kamar yadda Habibu Sodangi ya yi ikirari a X.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu na magana a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Saboda haka, masu binciken sun kammala cewa ikirarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta yaudara ce kuma ba ya nuna ainihin abin da Sultan ya faɗa.

Takardun Tinubu sun jawo muhawara

A wani labarin, mun ruwaito cewa wallafa takardun takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na zaɓen 2027 da hukumar INEC ta yi ya sake tayar da muhawara kan cancantar karatunsa.

Muhawarar ta ƙara ƙamari ne bayan an ga cewa babu bayanan takardun firamare da sakandare a cikin fom ɗin da aka wallafa, lamarin da jam'iyyun adawa suka ce yana buƙatar ƙarin bayani.

Sai dai wasu na ganin kotuna sun riga sun yanke hukunci kan irin wannan batu bayan zaɓen 2023, don haka bai kamata ya ci gaba da zama babban abin takaddama ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng