ICPC Za Ta Gurfanar da Tsohon Ministan Tinubu da Aka Samu da Takardun Bogi

ICPC Za Ta Gurfanar da Tsohon Ministan Tinubu da Aka Samu da Takardun Bogi

  • ICPC za ta gwabza da Uche Nnaji a kotu bisa zargin yin amfani da takardun bogi har ya zama minista a gwamnati
  • Lauyan hukumar ya shigar da kara a babban kotun tarayya mai zama a Abuja, yana zarginsa da aikata laifuffuka shida
  • Osuobeni Akponimisingha ya ce Nnaji ya samu kudi ta haramtaciyyar hanya kuma ya yaudari gwamnati ta takardun bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Hukumar ICPC mai yaki da rashin gaskiya za ta yi shari’a da Uche Nnaji wanda ya taba rike Ministan kirkira, kimiyya da fasaha.

Uche Nnaji ya rasa kujerarsa ne a sakamakon wannan badakala kuma tun lokacin ake zargin ya shiga wasan buya da hukumomin Najeriya.

Wani rahoto da ya kadaita da Premium Times ya nuna cewa ICPC ta shigar da karar Uche Nnajo a wani kotun tarayya mai zama a birnin Abuja.

Osuobeni Akponimisingha wanda lauyan ICPC ne, shi ya shigar da kara a madadin gwamnatin tarayya yana zargin Uche Nnaji da laifuffuka.

Kara karanta wannan

Sakataren APC da ya je kara a kotu ya dawo zai biya tarar Naira miliyan 100

Tuhuma shida ake yi wa Nnaji wanda yanzu haka yake neman takarar gwamnan Enugu a PDP.

A shari’ar da Osuobeni Akponimisingha ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/389/2026, Nnaji ne kadai wanda ake kara, zai kare kan shi a kotu.

Jaridar ta ce daga cikin zargin akwai mallakar N29,578,466.67 ta asusun bankinsa na Fidelity a matsayin albashi da alawus da yake minista.

Hukumar ICPC ta ce ya kamata Nnaji ya san cewa ya samu wadannan kudi ta haramtacciyar hanya.

Saboda haka aka ce an same shi da aikata laifin da ya sab awa sass ana 18(2)(d) da na 18(3) na dokar haramta juya kudi na shekarar 2022.

Ana tuhumar shi da amfani da ofishin minista wajen amfana ta hanyar da ba ta dace ba. Laifi na uku shi ne yaudarar gwamnati na bayanan karya.

ICPC ta ce takadar shaidar digiri mai lamba 004501 da ya gabatar na gaskiya kuma ya san da hakan, shi ma laifi ne da ya ci karo da dokar ICPC.

Lauya mai kara ya zarge shi da mika takardar kammala NYSC mai lamba No. A231309 wanda ya san na bogi ne, amma ya yi karyar akasin hakan.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shekara 1 da rasuwa an nemi a jefa Marigayi Buhari a shari'ar satar $6.2m

Laifi na karshe da ake tuhumarsa ita ce gabatar da takardar digirin jami’ar UNN, Nsukka da snan na gaskiya alhali ya san cewa takardar bogi ce.

Za a gurfanar da shi a kotu ne kusan mako daya bayan jami’an tsaro sun yi ram da shi a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a birnin Abuja.

ICPC: Jam'iyyar ADC ta yi magana kan El-Rufai

ICPC ta hana Nasir El-Rufai zuwa asibiti, ta kama likitansa, ta doki matarsa kamar yadda jam'iyyar ADC ta bayyana a wani jawabi da aka fitar ranar Talata.

Kakakin ADC ya ce sai da aka make wata matar tsohon gwamnan bayan ICPC ta kama likitansa kuma an hana shi zuwa asibiti kamar yadda kotu ta amince.

El-Rufai ya shafe watanni hannun hukuma ana binciken sa, sai dai Kakakin ADC na kasa ya bayyana cewa zalunci aka aikata ba yaki da rashin gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng