Tinubu ya yi watsi da kudirori 2 da majalisa ta aiko, ya ki sa hannu su zama dokoki

Tinubu ya yi watsi da kudirori 2 da majalisa ta aiko, ya ki sa hannu su zama dokoki

  • Bola Ahmed Tinubu bai gamsu da wasu kudirori da Majalisar tarayya ta aika masa ana neman sa hannunsa ba
  • Shugaban kasa ya rubuta wasika zuwa ga Godswill Akpabio dauke da kura-kuran da aka yi wajen aikin kudirorin
  • Idan an sake yin kwaskwarima, shugaba Tinubu ya fada wa majalisa a shirye yake ya amince kudirorin su zama dokoki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli 2026, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ki sa hannu a wasu kudirori da Majalisar tarayya ta aiko masa.

‘Yan majalisar tarayya sun gama aiki a kudirori biyu don haka aka bukaci sa hannun shi domin su zama dokoki, amma hakan ba ta samu ba.

Bola Tinubu
Mai girma Bola Tinubu a Eagles Square da wasu sanatoci a majalisa a shekarun baya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban Majalisa ya karanta wasikar Bola Tinubu

Jaridar This Day a wani rahoto ta ce shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya karanto wasiku mabanbanta da suka bayyana matsayar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Baki abin magana: Ndume ya yi fade fade bayan ganawa da Tinubu

A kudirin da ya nemi yi wa dokar da ta kafa hukumar RMRDC kwaskwrima, Bola Tinubu ya ce akwai kura-kuran da ya kamata a gyara su.

Meyasa shugaban kasa ya ki sa hannu a kudirorin?

Mai girma shugaban kasa ya ce akwai nakasu da aka samu wajen tsara kudirin wanda dole majalisa ta gyara kafin ya iya rattaba hannunsa a kai.

A wasikarsa, Tinubu ya ce dogon sunan da majalisa ta rada wa kudirin bai yi daidai da asalin abin da ya kunsa kuma yake nufin cin ma wa ba.

Abin bai tsaya a nan ba, shugaban na Najeriya ya ce kudirin ya yamutsa abubuwa biyu a wuri guda ga kuma wnai kuskure a cikin sashe na biyu.

Idan aka amince da garambawul din da aka yi, wasikar ta ce zai yi wahala dokar ta aiwatu a haka.

Jaridar Punch ta ce shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da kudirin cibiyar da ta ke kula da kwararru wajen harkar saye da samar da kaya a Najeriya.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ranar da aka rantsar da shi a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majalisa za ta yi wa kudirorin garambawul

Kara karanta wannan

Yadda Al Jazeera ta ba hadimin Tinubu hakuri a asirce kan wata hira da suka yi

Duk da shugaban na Najeriya ya ce wasu kwaskwariman da aka yi sun cancanci yabo, amma ya nuna akwai bukatar a sake yin wasu gyare-gyare.

Sai an yi wadannan gyare-gyare musamman a sashe na 11 na kudirin kafin ya amince ya zama doka.

Cibiyar ta bukaci a rika sanar da ita kafin yin wasu nadin-mukamai, Tinubu ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne a doka domin ba ta da wannan iko.

Da zarar an yi gyaran da ya nuna, shugaban kasar ya ce a shirye yake ya sa hannu. Nan da makonni hudu majalisar dattawa za ta gama aikin gyaran.

'Yan majalisa sun nemi cin hanci daga minista

Solomon Dalung ya fadi yadda suka buga da ‘yan majalisa da suka nemi ya biya su cin hancin N200m, amma a karshe suka shafa masa lafiya.

Kara karanta wannan

Matakai 4 da za a bi kafin tabbatar da 'yan sandan jihohi a Najeriya

An rahoto shi ya ce 'yan majalisa sun bukaci ya biya cin hancin N200m lokacin Muhammadu Buhari kafin a amince da kasafin kudin ma'aikatar shi.

Dalung ya ce ya fada wa kwamitin cewa tunda bai ga bangaren da aka rubuta "cin hanci" a takardar kasafin kudin ba, bai san inda zai nemo kudin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng