APC Ta Tabbatar da Canza Wasu ‘Yan Takara bayan Kammala Zaben Tsaida Gwani
- Felix Morka ya yi hira da manema labarai biyo bayan canjin ‘yan takaran da aka samu a jam’iyyar APC
- Kakakin na jam’iyya mai mulki ya ce korafin da aka samu bayan zabe ya haifar da sauye-sauyen ‘yan takara
- Sakataren yada labaran na APC ya ce tuni sun fara kokarin lallashin wadanda yanzu suka rasa tutar takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka, ya tabbatar da cewa an sauya sunayen wasu ‘yan takara bayan zaben tsaida gwani.
Felix Morka ya bayyana cewa babu wani mai neman takara da bai shiga zabe ba wanda aka ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara a jam’iyyar.

Source: Facebook
Jam'iyyar APC ta yi wa jerin 'yan takara garambawul
Kakakin na APC ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise a ranar Talata sakamakon surutan da suka biyo sauyin 'yan takaran.
APC ta karyata cewa ta rika daukar takara ne kurum tana mika wa wadanda ba su shiga zabe ba.
A hirar da aka yi da shi, Morka ya yi bayanin yadda uwar jam’iyya ta karbi korafi fiye da 720 bayan zaben tsaida gwanin da APC ta gudanar a kwanaki.
Mista Morka ya ce sauye-sauyen da aka samu a sakamakon shawarwarin da kwamitin sauraron korafi ya kawo ne da kuma aikin da uwar jam’iyya ta yi.
"A karshen duka wadannan, mun yi wadannan sauye-sauye da ku ke magana a kai. Saboda haka wadannan korafi ne masu tushe daga zaben tsaida gwaninmu.
“Ban da masaniyar irin abubuwan da ku ke ikirari cewa wadanda ba su shiga zabe, wadanda ba su saye fam ba, ba a tanance su ba, ba su shiga takara ba gaba daya, aka ce an damka masu tikiti.”
- Felix Morka
Punch ta ce jam’iyyar APC ta karyata zargin da ake yi cewa an saba dokar zabe wajen canza ‘yan takaran, ta ce doka ta bada hurumin wannan sauyi.
APC tana ba masu neman takara hakuri
An ji Morka yana bayanin kokarin da jam’iyya ta ke yi na ba wadanda aka hana takara hakuri, ya ce babu wani da APC ta ke neman ganin bayan shi.
Kafin a cin ma wata matsaya, uwar jam’iyya ta ce sai da kwamitin gudanarwa ya zauna a kan korafin da masu neman a tsaida su, suka mika mata.

Source: Facebook
A cewarsa, ana kokarin kwantar da hankalin wadanda ba su yi nasara ba, ana kokarin gamsar da su cewa ba son rai aka yi wajen maye gurabensu ba.
"Abin da muka fada masu shi ne ba za ta yiwu kowa ya samu tuta ba. Muna tattaunawa yanzu haka da daidaikunsu, mu tabbatar masu cewa ba a kullaci kowa ba.
"Babu abin da aka yi da ya saba ka’ida. Babu wanda aka fifita wajen samun tikiti."
- Kakakin APC
APC ta cafko kusa a tafiyar Atiku Abubakar
Wata mutumiyar Atiku Abubakar ta tsawo shekaru 20 ta yi sallama da shi. An ji labarin dalilin shigar ta APC duk da shakuwar ta da jagoran adawar kasar.
Gimbiya Aslam Aliyu, matar da ta shafe shekara da shekaru tare da Atiku Abubakar a siyasa ta bi layin Bola Tinubu, ta ce shi zai zabe a shekara mai zuwa.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya tarbi 'yar siyasar wanda dama can an yi ta rade-radin za ta canza gida.
Asali: Legit.ng


