Babban Darakta a Kannywood Aminu Saira Ya Yi Sabon Aure, Hotunan Matansa Sun Jawo Cece Kuce
- Fitaccen mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood, Malam Aminu Saira, ya ƙara aure a jihar Bauchi
- Abokan aikinsa, masoya da masu ruwa da tsaki a Kannywood sun halarci ɗaurin auren na sa da amaryarsa
- Hotunan Malam Aminu Saira tare da matansa biyu sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan an yada su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Azare, Bauchi - Fitaccen mai shirya fina-finai kuma daraktan Kannywood, Malam Aminu Saira, ya auri mata ta biyu a wani ɗaurin aure mai kayatarwa da aka gudanar ranar Juma'a a garin Azare, jihar Bauchi.
Ɗaurin auren ya samu halartar abokan aikinsa, masoya da masu ruwa da tsaki a masana'antar fina-finai daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta fahimci cewa an daura auren Malam Aminu Saira ne a ranar Juma'a, 31 ga watan Yulin 2026.
Mutane da dama sun kuma cika kafafen sada zumunta da saƙonnin taya daraktan murna bisa sabon auren da ya yi.
Aminu Saira ya yi godiya
A wani sako a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 1 ga watan Yulin 2026, Aminu Saira ya yi godiya kan wadanda suka halarcu auren nasa da masu yi masa addu'o'i.
"Ina mika sakon godiya ga “yan uwa da abokan arzuka da suka halarci bikin aure na a garin Azare dake Jihar Bauchi, sannan ina mika godiya ga mutanen da basu samu damar halar ta ba suka taya mu da addu’a. Allah ya sakawa kowa da alkhairi, Allah kuma yabar zumnci.... Amin. Mu kuma Allah ya bamu ikon yin adalci ga Matan mu kamar yadda addini mu yayi umarni... Amin 1Love❤️🌎🙌"
Hotunan matan Aminu Saira sun yaɗu
Bayan kammala ɗaurin auren, hotunan Aminu Saira tare da matansa biyu suka fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
Yaduwar hotunan ta jawo tattaunawa tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta kan batun auren mata fiye da ɗaya da zaman lafiya a cikin iyali.
Wasu daga cikin masu sharhi da masoyansa sun yi amfani da dandamali daban-daban wajen yaba wa Saira saboda yadda yake tafiyar da harkokin gidansa a bayyane.
Me mutane ke cewa kan matan Aminu Saira?
Sabon auren da Aminu Saira ya yi ya ja hankalin masoyansa da sauran masu bibiyar harkokin Kannywood, musamman bayan da hotunansa tare da matansa biyu suka bazu a intanet.
Sany Muhammad Ubale ya rubuta:
"Wato mutum dai koyanada iPhone tsabar karanbani sai yahada da vivo"
Abdoolberqee Moosterpha ya rubuta:
"Koh meh sa basa auran yan film? "Kuma sunce tarbiya suke koyarwa, kuma basa auran wa'enda suke tarbiyantarwa"
Kabiru Danjuma ya rubuta:
"Duk Wanda ya lura amarya a firgice ta ke yai mun like"
Muhd Auwal Xango ya rubuta:
"Namiji Mai leqe leqe, kanada s 26 ultra, katafi yen Vivo. Allah yabada zaman lafiya."
Abdullahi Muhammad Wuna ya rubuta:
"Ma sha Allah! Amma maganar gaskiya Uwargidan tafi Amaryar...."
Suheeb Cherky Lucky ya rubuta:
"Kanada iPhone ka siyo vivo Allah ya kyauta"

Source: Facebook
Adam Zango ya saki matarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Adamu A. Zango, ya saki matarsa, jaruma Maimuna Pretty.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa tsohuwar jaruma Maimuna ta kwashe kayanta daga gidan Adam A Zango bayan rabuwarsu.
Asali: Legit.ng


