Lokaci Ya Yi: Babban Malami a Jami'ar ABU Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Dr. Umar Sani Bebeji ya rasu sakamakon wani mummunan hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya
- Marigayin malami ne a sashen tsangayar shari’a na kasuwanci da ke Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria
- An bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda rashinsa ya girgiza mutane masu yawa saboda kyawawan halayensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Zaria- Wani babban malami a Tsangayar Koyon Shari’a ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, Dr. Umar Sani Bebeji, ya rasu sakamakon wani mummunan hadarin mota.
Wani abokin marigayin tun suna yara kuma abokin aikinsa a Tsangayar Fasaha ta ABU, Zubairu Lawal Bamalle, ya tabbatar da rasuwarsa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Bamalle ya ce hadarin ya faru ne a Dumbin Rauga da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026.
Dr. Bebeji ya bar iyali
Marigayin ya rasu yana da shekara 45 a duniya, ya bar mata daya da yara biyu.
Duk da cewa sunansa ya samo asali ne daga Bebeji da ke jihar Kano, Dr. Bebeji ya shafe dukkan shekarun yarintarsa a Tudun Wada da ke Kaduna. An binne shi a makabartar Kwanar Chanchangi da ke Kaduna.
Mukamansa a jami’ar ABU
Dr. Bebeji babban malami ne a Sashen Shari’a na Kasuwanci da ke Tsangayar Koyon Shari’a ta ABU.
Ya kuma taba rike mukamin mataimakin shugaban tsangayar, sannan ya kasance mai kula da ABU Law Clinic.
A matsayinsa na mai kula da cibiyar, ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen bunkasa koyar da shari’a ta hanyar aiki da kuma taimaka wa al’ummomin da ba su da isasshen damar samun adalci.
Dalibansa da abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin hazikin masani, malami mai tawali’u kuma kwararren lauya mai jajircewa.
Sun ce za a dade ana tuna gudummawar da ya bayar wajen bunkasa ilimin shari’a.
Jama'a sun yi alhini
Hauwa Sani ta bayyana alhininta tare da yi wa marigayin addu’a.
“Ya Allah! Ka ji kan Umar Sani Bebeji, Ka gafarta masa, Ka shigar da shi Aljannarka. Ya kasance mutum nagari. Allah Ya yafe masa kura-kuransa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi. Hasbunallahu wa ni’imal wakil.”
Hannatu Shehu Tarfa ma ta bayyana bakin cikinta kan rasuwar.
“Allah Ya ji kansa. Allah Ya sa makomarsa Aljannatul Firdaus. Allah Ya gafarta masa dukkan zunubansa. Zuciyata ta yi matukar nauyi.”

Source: Facebook
'Ya'yan tsohon mataimakin gwamna sun rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa 'ya'yansa biyu a wani mummunan hatsarin mota.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce yana jajanta wa Sanata Baba Tela bisa rasuwar ƙaunatattun 'ya'yansa, Mustapha da Ummi, da suka mutu a hatsarin mota.
Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ya karɓi labarin cikin matuƙar kaɗuwa da baƙin ciki, yana mai cewa wannan babban abin takaici ne ga Bauchi.
Asali: Legit.ng

