Jam'iyyar PDP Ya Zabi Mutumin da Zai Yi Mata Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027
- Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed ta bayyana Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ne ya sanar da sakamakon zaɓen fitar da gwani a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja
- INEC ta sanya ido kan taron yayin da PDP ta miƙa wa Sandy Onor tutar jam’iyya da takardar shaidar nasara a zaben fitar da gwanin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed ta bayyana tsohon ɗan takarar gwamnan Cross River, Sanata Sandy Onor, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasarta na zaɓen 2027.
An sanar da hakan ne ranar Talata yayin tattara wa da bayyana sakamakon zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da aka gudanar a Wadata Plaza da ke Abuja.

Source: Facebook
Onor ya zama dan takarar PDP
Shugaban kwamitin tattara sakamakon zaɓen fitar da gwani kuma tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ne ya bayyana hakan yayin taron, in ji rahoton Chennels TV.
Mambobin kwamitin sun ce an gudanar da zaɓen ne bayan tattaunawa da kada ƙuri’ar baki da aka yi da mambobin jam’iyyar a jihohi daban-daban.
Rahotanni sun nuna cewa Sandy Onor ne kaɗai ya tsaya takarar shugaban ƙasa bayan ya sayi fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara a farkon watan nan.
Yadda PDP ta zabi dan takara
Da yake jawabi yayin taron, Ortom ya ce kwamitin ya tattauna da mambobin jam’iyyar daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja kafin cimma matsayar tsaida Sandy Onor.
Daga bisani ya ayyana Sanata Sandy Onor a hukumance a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP domin babban zaɓen shekarar 2027, in ji rahoton Punch.
INEC ta sanya ido
Kwamishinonin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Abdullahi Zuru da Farfesa Rhoda Habor Gumus, tare da wasu jami’an hukumar, sun sanya ido kan taron a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa.
Bayan sanarwar, shugabannin PDP sun miƙa wa Sanata Sandy Onor takardar shaidar nasara da kuma tutar jam’iyyar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Source: Facebook
PDP ta taya Jonathan murna
Wannan na zuwa ne awanni bayan, PDP ta yi martani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya tabbatar da cancantar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
PDP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar, Ini Ememobong, ya sanya wa hannu ranar Talata kuma aka wallafa a shafin jam'iyyar na X.
Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren PDP mai alaƙa da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya amince da Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasarsu a zaɓen 2027.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Kotu ta yi hukunci kan takarar Jonathan
A wani labari, mun ruwaito cewa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci game da karar da aka shigar gabanta na neman hana tsohon shugaban kasa takara a 2027.
Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya nemi kotu ta hana Jonathan shiga takara, amma kotun ta yi watsi da bukatar a hukuncin da aka yanke a yau.
Mai shari'a Peter Lifu ya hukunta cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai hana Jonathan sake neman kujerar shugaban ƙasa ba duk da yunkurin wasu na hana hakan.
Asali: Legit.ng


