Komai Ya Fito Fili, INEC Ta Saki Bayanan Karatun Tinubu da Shettima
- Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta fara fitar da bayanan karatun masu neman takarar shugaban kasa da mataimakansu
- Hukumar ta ce matakin ya yi daidai da tanadin Sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026 yayin da ake kara daura damara domin zaben 2027
- Hukumar ta nemi jama'a su taya ta duba bayan da ke cikin takardun, tare da ɗaukar matakin shari'a idan sun gano bayanan ƙarya a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara nuna takardun shaidun karatu da bayanan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.
Wadannan bayanai da aka fitar su ne wanda yan takarar suka gabatar domin tsayawa takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa a ƙarƙashin jam'iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa hukumar ta bayyana cewa an fara wannan tsari ne a ranar Asabar 1 ga watan Agusta, 2026 bisa tanadin Sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026.
Mun bi doka ne - INEC
Jaridar Punch ta wallafa cewa dokar da ta yi umarni da a wallafa bayanan masu neman takara ya wajabta yin hakan a cikin kwanaki 21 bayan karɓar takardunsu.
A cewar INEC:
"Fom EC9 na ɗauke da takardun shaidar karatu, bayanan sirri da kuma takardun rantsuwar da 'yan takarar da jam'iyyunsu suka gabatar."
Takardun da aka rataya a ofisoshin INEC na faɗin ƙasar sun nuna tarihin karatu da aikin Shugaba Tinubu. A cikin fom ɗinsa na EC9, an bayyana cewa ya samu digiri a fannin Business Administration daga jami'ar a Amurka, inda aka ba shi digirin tare da karramawa a ranar 22 ga Yunin 1979.
Takardun sun kuma nuna bayanan hidimarsa ta NYSC, inda ya yi bautar ƙasa a jihar Oyo daga watan Disamban 1982 zuwa Nuwamban 1983.
Game da tarihin aikinsa, an bayyana cewa ya yi aiki a Mobil Nigeria Limited daga 1983 zuwa 1992 kafin ya bar aiki domin ci gaban rayuwarsa. D
aga nan ya zama gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 da 2007, sannan tun shekarar 2023 yake shugabantar Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
INEC ta fitar da bayanan Kashim
Takardar shaidar kammala firamare da tsohuwar Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Arewa maso Gabas ta bayar ta nuna cewa ya yi karatu a firamen Lamisula I Primary tsakanin 1972 zuwa 1978.

Source: Facebook
Daga bisani ya kammala digiri a fannin aikin gonada sakamako na Second Class Upper daga Jami'ar Maiduguri a watan Agustan 1989, sannan ya samu digirin Master of Science a fannin Agricultural Economics daga Jami'ar Ibadan.
Takardun NYSC nasa sun nuna cewa ya yi bautar ƙasa daga Oktoban 1989 zuwa Oktoban 1990. INEC ta jaddada cewa jama'a na da damar neman kwafin sahihan takardun fom ɗin takarar da sauran bayanan da 'yan takara suka gabatar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa duk wanda ya yi zargin an bayar da bayanan ƙarya ko kuma an yi amfani da jabun takardu na iya neman hakkinsa ta hanyar kotu.
'Yan daba sun mamaye jami'an INEC
A baya, mun kawo labarin cewa wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari cibiyar rabon katin zaɓe ta INEC da ke jihar Osun tare da kwashe wasu katunan zaɓe na dindindin (PVC).
Maharan sun harba bindiga sama domin tarwatsa jama'a kafin su tsere da katunan PVC, lamarin da ya jefa mutane cikin firgici ganin yadda ake kara kusanto zaben gwamnan jihar a watan nan.
Rundunar 'yan sandan Osun ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an fara bincike domin kamo waɗanda suka kai harin tare da ƙwato katunan da aka sace yayin da hukumar INEC ke bayar da tabbacin sahihin zabe.
Asali: Legit.ng


