INEC na Shirin Cire NDC daga Rajistar Jam’iyyun Siyasa bayan Hukuncin Kotu

INEC na Shirin Cire NDC daga Rajistar Jam’iyyun Siyasa bayan Hukuncin Kotu

  • Hukumar INEC ta ce za ta sake duba matsayin NDC bayan wata babbar kotun jiha ta soke hukuncin da ya tilasta mata yi wa jam’iyyar rajista
  • Wata kotun tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi ta ce hukuncin baya ya shafi hakkokin wata jam’iyya da ba a shigar da ita cikin karar ba
  • Hukumar INEC ta ce za ta yi aiki da sabon hukuncin kotu bayan ta samu kwafin hukuncin da aka tabbatar da soke rajistar NDC da ta yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa tana shirin cire NDC daga rajistar jam’iyyun siyasa bayan wata babbar kotun tarayya ta soke hukuncin da ya tilasta mata yin rajistar jam’iyyar.

INEC ta bayyana hakan ne bayan kotun ta soke hukuncin da aka yanke a watan Disambar 2025 wanda ya umarci hukumar ta amince da NDC a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, NDC ta bayyana makomar takarar Peter Obi da Kwankwaso a zaben 2027

INEC ta ce tana shirin soke rajistar jam'iyyar NDC bayan hukuncin kotu
'Dan takarar shugaban kasa Peter Obi yana daga tutar jam'iyyar ADC a taron kaddamar da takararsa. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

INEC ta yi magana kan rajistar NDC

Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar ta nemi kwafin hukuncin da aka tabbatar (CTC) domin daukar matakin da ya dace, in ji rahoton Vanguard.

Ya ce:

“Mun nemi kwafin hukuncin da aka tabbatar. Har sai mun same shi, ba za mu iya yin tsokaci a kai ba.”

Ya kara da cewa kafin hukuncin ranar 10 ga Disambar 2025, INEC ta ayyana cewa ba za ta amince da bukatar NDC na yi mata rajista matsayin jam’iyyar siyasa ba.

Hukuncin da kotu ta yanke kan NDC

Mai shari’a Isah Dashen na Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ne ya soke hukuncin baya a ranar Juma’a, yana mai cewa hukuncin ya shafi hakkokin wata jam’iyya mai suna PMP.

Kotun ta bayyana cewa ba a shigar da PMP cikin karar ba duk da cewa tana ikirarin mallakar tambarin da NDC ta yi amfani da shi wajen neman rajistar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Najeriya ta yanke wa Ibrahim da Abdullahi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Lauyan PMP, C. S. Ekeocha, ya ce hukuncin kotun ya rusa dukkan matakan da aka dauka sakamakon hukuncin baya, cewar rahoton The Guardian.

Hukumar INEC ta ce za ta dauki mataki kan soke rajistar NDC da zarar ta samu cikakken kwafin hukuncin kotu.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan yana jawabi. Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

PMP ta nemi a soke rajistar NDC

A cewarsa, ya kamata a janye rajistar NDC, bayar da takardar shaidar rajista, saka sunan jam’iyyar a bayanan INEC da kuma duk wani bayyanar da ta yi a katin zabe ko takardar kuri’a har sai an kammala shari’ar.

Lauyan PMP ya kuma bayyana cewa babbar shari’ar da ta haifar da rikicin har yanzu tana gaban kotu kuma ba a yanke hukunci a kanta ba.

Yanzu haka ana sa ran INEC za ta dawo da tsohon matsayin da ake ciki kafin hukuncin Disambar 2025, har sai kotu ta kammala sauraron karar gaba daya.

BDC ta magantu bayan hukuncin kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, NDC ta yi fatali da hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Lakoja, wanda ya rusa rijistar da aka mata a matsayin jam'iyyar siyasa.

NDC ta tabbatar wa Peter Obi, Kwankwaso da sauran 'yan takararta cewa hukuncin ba zai hana jam'iyyar shiga babban zaben 2027 ba.

A sanarwar da ta fitar yau Juma'a, jam’iyyar NDC ta ce ta umarci lauyoyinta su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com