2027: 'Yan Takarar NDC Sun Gamu da Matsala bayan INEC 'Ta Hana' a Shigar da Sunayensu
- Jam'iyyar NDC ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kokarin jawo wa 'yan takararta matsala a babban zaben 2027 da ke tafe
- NDC ta bayyana wannan sabon kalubale ne bayan wata kotu da ke Lokoja a jihar Kogi ta taka wa hukumar INEC yi wa jam'iyyar rajista gabanin zaben
- Duk da wannan hukunci na Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, NDC ta dage cewa har yanzu ita jam'iyya ce mai rajista kuma za ta tsayar da 'yan takara a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar adawa ta NDC ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu lambar da za ta ba ta damar shigar da sunayen 'yan takararta a shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ba. Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Osa Director da ya bayyana haka ya kara da cewa sun riga sun aika bukata ga INEC domin samun lambar, amma har yanzu hukumar ba ta ba su amsa ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tuni ta fitar da sunayen wadanda za su tsaya mata takara a babban zabe mai zuwa, kuma babu abin da zai hana ta shiga a fafata da ita a 2027.
NDC ta yi kuka da INEC
Jairdar Daily Post ta kawo labarin cewa Mai magana da yawun NDC na ƙasa, Osa Director, ya ce jam’iyyar ta je INEC domin karɓar lambar da ake buƙata kafin a kammala shigar da sunayen ’yan takara ta yanar gizo, amma ba ta samu ba.
A cewarsa, jami’an hukumar zaɓen sun shaida musu cewa za su sake tuntuɓarsu daga baya, lamarin da ya hana jam’iyyar kammala loda sunayen 'yan takara kafin hukuncin kotun na soke rajistar ya fito.
Ya ce:
"Mun je INEC domin karɓar lambar shiga da za mu yi amfani da ita wajen loda sunayen ’yan takararmu a manhajar INEC. Sun ce za su dawo gare mu."
NDC ta sake garzaya wa INEC da kotu
Osa Director ya jaddada cewa rashin loda sunayen ’yan takarar bai faru saboda gazawar jam’iyyar ba, yana mai cewa jinkirin ya samo asali ne daga rashin ba su lambar shigar da sunayen da suke buƙata daga INEC.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya kuma bayyana cewa NDC za ta sake komawa INEC domin yin sabon ƙoƙarin samun lambar shigar da sunayen, tare da ɗaukar matakin shari’a domin dakatar da aiwatar da hukuncin kotun da ya ba da umarnin soke rajistarta.

Source: Twitter
A cewarsa:
"Za mu sake komawa can gobe. Na yi imanin cewa zuwa gobe za mu kasance mun shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin kotu."
'Dan takarar NDC ya dura a kan Tinubu
A baya, mun wallafa labarin cewa 'dan takarar shugaban kasa a NDC, Mr. Peter Obi ya zargi gwamnatin APC a karkashin Bola AhmedTinubu da kokarin hana shi rawar gaban hantsi yayin da ake shirin zaben shekarar 2027.
Tsohon gwamnan ya kalubalanci masu neman shugabancin kasa, har da Tinubu, da su fito muhawara su bayyana shirinsu ga Najeriya domin jama'a su samu damar tantance wa tsakanin awa da tsakuwa.
Obi ya ce ba son mulki ke tura shi neman takara ruwa a jallo ba, sai dai burin ganin Najeriya ta gyaru, yana mai kira ga matasa su karbi katin zabe domin su dangwala wa 'yan takarar da suka cancanta a babban zaben.
Asali: Legit.ng


