Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Nemi Tallafin ECOWAS na Dala 65,000
- Ƙungiyar ECOWAS ta buɗe shafin neman tallafin kasuwanci na karo na biyu, inda za a raba kyaututtukan kuɗi da suka kai $65,000 ga sabbin kamfanoni
- Shirin ya shafi ‘yan Najeriya da sauran ‘yan ƙasashen ECOWAS masu kamfanonin fasaha da ke da sababbbin dabaru da kuma damar bunƙasa kansu
- Rahotanni sun nuna cewa masu neman tallafin za su iya gabatar da bayanan su ga ECOWAS daga ranar 3 ga Agusta zuwa 31 ga Agusta, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta buɗe shirin neman tallafi na karo na biyu ga sababbin kamfanoni daga ƙasashen yankin, ciki har da Najeriya.
Shirin zai raba kyaututtukan kuɗi da suka kai $65,000 tare da samar wa waɗanda aka zaɓa damar samun horo, haɗin gwiwa da tallafin bunƙasa kasuwancinsu.

Kara karanta wannan
Zaben Osun: Saura kwana 5 a fara kada kuri'a, an bankado makarkashiyar da ake kullawa

Source: Facebook
Yaushe aka buɗe neman tallafin?
ECOWAS ta buɗe neman tallafin ranar 3 ga Agusta, 2026, kuma za a rufe shafin karɓar bayanai a ranar 31 ga Agusta, 2026 kamar yadda ta wallafa a X.
Za a gudanar da wasu darussan ƙwarewa ta yanar gizo daga 21 zuwa 25 ga Satumba, kafin a gudanar da taron kai tsaye a Abuja daga 28 zuwa 30 ga Satumba.
Za a kammala shirin da babban taron ƙarshe na yankin a Abuja ranar 30 ga Satumba, 2026.
Shirin na neman kamfanoni 60 daga cikin ƙasashen ECOWAS guda 12 da za su fafata a fannoni daban-daban na fasaha da kasuwanci.
Nawa za a ba mutane?
Punch ta wallafa cewa wanda ya zo na farko zai samu kyautar $20,000. Wanda ya zo na biyu zai samu $15,000, yayin da shirin zai samar da wasu fa'idodi ga waɗanda aka zaɓa.
Daga cikin fa'idodin akwai samun damar bayyana kasuwanci a ƙasashen ECOWAS, haɗuwa da masu zuba jari da kuma shiga shirye-shiryen horo da jagoranci na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan
'Dalilin da ya kamata ya sanya hukumar INEC ta gudanar da zaben 2027 a rana guda'

Source: Facebook
Sharuddan da za a cika
Mai neman tallafin dole ne ya kasance ɗan ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS, ciki har da Najeriya kuma dole ne kamfanin ya kasance yana da rajista kuma yana aiki a ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS.
An ce ya kamata kamfanin ya kasance yana aiki aƙalla shekaru biyu, tare da samun samfur ko sabis da yake aiki.
Dole ne mai nema ya nuna cewa kamfaninsa yana da kwastomomi ko damar faɗaɗa kasuwa, tare da gabatar da dukkan takardun da ake buƙata.
Ana ba matasa tallafin karatu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Tunde Onakoya, ya haɗa gwiwa da wanda ya kafa Jobs59, Sam Otigba, da wanda ya kafa ALT, HackSultan, wajen ƙaddamar da asusun tallafin karatu na Naira miliyan 250.
Shirin zai bai wa waɗanda aka zaɓa tallafin N160,000 domin yin karatun diploma a AltSchool tare da samun taimakon neman aiki da damar koyon sana'a a kamfanoni.
Wasu daga cikin waɗanda za su amfana za su kuma samu kwamfutoci kyauta domin taimaka musu wajen koyon ƙwarewar fasaha da samun damar neman aiki.
Asali: Legit.ng