An Gano Adadin Jami'an Tsaro da Ƴan Ta'adda da Suka Mutu a Arangamar Kebbi

An Gano Adadin Jami'an Tsaro da Ƴan Ta'adda da Suka Mutu a Arangamar Kebbi

  • Rundunar 'yan sanda ta ce ta kashe ’yan bindiga 17 yayin wata arangama da jami’an tsaro a yankin Rafin Makuku na Jihar Kebbi.
  • Sai dai duk da nasarar da aka samu, an samu jami'an rundunar da dama sun kwanta da wasu mutum biyu daga cikinsu suka samu raunuka
  • Mazauna sun ce ’yan bindigar sun kai kimanin 240, dauke da babura sama da 200, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da farautar wadanda suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – ’Yan bindiga 17 da jami’an ’yan sanda 10 ne aka kashe ranar Litinin 10 ga watan Agusta, 2026 yayin da jami’an tsaro suka yi arangama da gungun ’yan bindiga a Kebbi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zugar 'yan ta'addan dauke da makamai sun yi arangama da jami'ai a jihar Kebbi bayan sun taso daga Zamfara.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

An kashe yan sanda 10 a Kebbi
Sufeto Janar na yan sandan Najeriya Tunji Disu Hotoo; Nigeria Police Force
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa rikicin ya faru ne a yankin Rafin Makuku da ke Karamar Hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi, inda fararen hula biyu suka rasa rayukansu, a cewar ’yan sandan jihar.

Yadda aka buga da yan ta'adda a Kebbi

A ruwayar Daily Post, mazauna yankin sun ce ’yan bindigar, wadanda adadinsu ya kai kusan 240, sun yi amfani da babura sama da 200 wajen tafiya daga yankin Sangeko Gap da ke Gundumar Dansadau a Karamar Hukumar Maru ta Zamfara.

Wani mazaunin Makuku, Malam Musa Sani, ya ce ’yan bindigar sun rabu gida uku kafin su yada zango a wani daji tsakanin Kakihum da Makuku, inda suka kwana kafin su nufi Maburya da safiyar Litinin 10 ga watan Agusta, 2026.

Musa Sani ya ce ’yan bindigar sun ci karo da wani shingen ’yan sandan Mopol yayin da suke kokarin shiga garin, inda suka yi galaba a kansu.

Yan sanda sun yi magana kan artabun Kebbi

Kara karanta wannan

"Mun bar ku da Allah': Mazauna Sokoto sun tura sako ga Gwamna kan rashin tsaro

Da yake tabbatar da harin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Bashir Usman, ya ce kawo yanzu an tabbatar da kashe ’yan bindiga 17.

An kashe yan ta'adda akalla 17 a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi inda aka yi arangama da yan ta'adda Hoto; Legit.ng
Source: Original

Bashir Usman ya ce jami’an tsaro sun tare tare da bude wuta kan gungun ’yan bindiga dauke da makamai” da ke kokarin wucewa tsakanin Zamfara da Kebbi a yankin Rafin Makuku.

Ya ce an kona babura hudu na ’yan bindigar a yayin arangamar, amma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa ko sauyawa yayin da ake ci gaba da tantance bayanan.

Ya ce:

“Abin takaici, mun rasa jajirtattun jami’an ’yan sanda 10 a arangamar, yayin da wasu biyu suka samu raunuka kuma suke karbar magani. Fararen hula biyu ma sun rasa rayukansu."

Da ya ke yi wa Legit karin bayani, wani mazaunin yankin Zakari Ya'u ya shaida cewa wadanda abin ya faru a kan idonsu sun ce an kashe fararen hula biyu nan take.

"Yan sandan kwantar da tarzoma wato Mopol ke nan sun samu labari inda suka zo suka masu kwanton bauna a bakin garin daidai wurin da za ka shiga cikin gari da ya ke akwai rafi da ya raba bangaren Neja da Kebbi."

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

"Suna dab da za su shiga garin Makuku wadannan jami'an tsaron duk da ba su da yawa, amma haka suka tunkare su aka yi kazamin fada kuma an samu galaba sosai."

Zakari ya ce amma karancin jami'an tsaro ya taimaka wajen rasuwar zaratan yan sandan da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare mutanen gari.

An tarwatsa yan ta'adda a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa sojojin birged na 17 na rundunar sojin Najeriya sun hango taron ’yan bindiga da ke shirin kai hari karamar hukumar Charanchi ta Jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.

Rundunar ta samu kiran gaggawa da 11.20 na safe, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga sun taru a kusa da kauyen Kaddanya a wani yunkuri na kai wa bayin Allah hari.

Sojojin sun gudanar da sintiri mai razana zuciyar masu aikata laifi tare da mamaye yankin bayan sun dauki matakin korar 'yan bindigar tare da kwace makamai masu tarin yawa daga hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng