Da Gaske Obi Ya Ce Sojoji Su Yi wa Tinubu Bore kan Albashi?

Da Gaske Obi Ya Ce Sojoji Su Yi wa Tinubu Bore kan Albashi?

  • Peter Obi ya musanta rahoton da ke cewa ya nemi sojojin Najeriya su ƙi karɓar ƙarin albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi
  • Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce rahoton ƙarya ne, yana mai kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da shi gaba daya
  • Obi ya ce zai bai wa jin daɗin sojoji, tsaro, kayan aiki da martabar jami'an tsaro muhimmanci idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya musanta rahoton da ke cewa ya nemi sojojin Najeriya su ƙi amincewa da ƙarin albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi.

Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, yana mai kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Wuta ta yi wuta: Babban sojan Amurka na neman a fita a yaki da Iran

Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi. Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Peter Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.

Bayanin da Obi ya yi

Obi ya ce wani rahoto ya danganta masa kalaman da bai taɓa yi ba, inda aka ce ya nemi sojoji su ƙi karɓar ƙarin albashi har sai bayan zaɓe.

Ya ce:

"Ina son yin bayani kan wani rahoto da ya danganta mini da wani bayani na ƙarya, cewa sojojin Najeriya su ƙi duk wani ƙarin albashi har sai bayan zaɓe. Wannan magana ba gaskiya ba ce."

Jaridar Punch ta wallafa cewa Peter Obi ya buƙaci jama'a da su yi watsi da rahoton da ya kira abin yaudara.

Obi ya ce yana girmama sojoji

Obi ya ce yana matuƙar girmama jami'an tsaro, musamman sojojin Najeriya da ke aiki wajen kare ƙasa a cikin mawuyacin hali.

Ya ce:

"Babban girmamawa da nake yi wa jami'an tsaronmu, musamman sojojin Najeriya da ke aiki tukuru wajen kare ƙasarmu a cikin mawuyacin yanayi, ba zai canza ba."

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

A sanarwar ta ya fitar, Obi ya ce ya daɗe yana kira da a samar wa jami'an tsaro isassun kayan aiki, ƙarfafa musu gwiwa da kuma kariya.

Obi ya tuna da sojoji

Tsohon gwamnan Anambra ya tuna da wani lamari da wasu sojoji suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan tawaye.

Ya ce lamarin ya sa ya yi tambaya kan yadda ake kare jami'an da ke sadaukar da rayukansu wajen kare Najeriya.

Obi ya ce:

"Damuwata ta bayyana sosai lokacin da aka rasa sojoji sakamakon jinkirin kai musu ɗauki, abin da ya sa na tambayi yadda za a bar waɗanda ke kare mu cikin haɗari a lokacin da suke buƙatar taimako."
Hafsun sojin kasan Najeriya
Hafsun sojojin kasa, Lafatanar Janar Waidi Shuaibu a jihar Rivers. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Sabun albashin sojoji a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa sabon tsarin albashin jami'an Rundunar Sojin Najeriya da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi zai kai albashin Janar zuwa Naira miliyan 3.25 a wata.

A ƙarƙashin sabon tsarin, albashin soja mai matsayi na Private zai kai Naira 187,200 a wata, yayin da ƙarin albashin zai kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100.

Sabon tsarin zai amfanar da kusan jami'an tsaro 250,000, tare da ƙara kuɗin albashin shekara-shekara na Rundunar Sojin Najeriya daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng