'Yan Bindiga Sun Kai Hari Katsina, Sun Tafka Barna Mai Girma
- 'Yan bindiga sun kai hari Unguwar Aminu da ke Kandarawa a jihar Katsina, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu huɗu da harbin bindiga
- Maharan da ke dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu mutane tare da kwashe dabbobi da kuma fasa shaguna
- Mazauna garin sun fara barin gidajensu saboda fargabar sake kai musu harin 'yan bindiga wadanda suka addabe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kai hari Unguwar Aminu da ke Kandarawa, a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyu, suka sace wasu mutane shida tare da jikkata huɗu da harbin bindiga a daren Talata, 11 ga watan Agustan 2026.

Source: Original
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa harin ya kuma kai ga satar wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba, yayin da maharan suka fasa wasu shaguna tare da kwashe kuɗi, wayoyin hannu da sauran kayayyaki masu daraja.
An binne mutum biyu da aka kashe
An bayyana waɗanda aka kashe a harin da Ibrahim Sama’ila da Mashakuru Isa. An yi jana’izarsu tare da binne su bisa tsarin addinin Musulunci a safiyar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026.
A yayin harin, maharan sun yi awon gaba da maza uku da mata uku, yayin da aka garzaya da mutane huɗu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Mazauna yankin sun bayyana abin da ya faru
Mazauna yankin sun ce tun da farko sun hangi maharan suna tafiya gabas daga Doma, a ƙaramar hukumar Faskari, amma daga baya suka ɓace kafin su bayyana ba zato a Unguwar Aminu.
Mafarauta da sauran ƙungiyoyin tsaro sun tattara kansu domin tunkarar maharan da kare al’ummar garin, amma 'yan bindigar sun tsere.
Mata da yara sun bar garin
Bayan harin, an ga mata da yara da dama suna barin garin zuwa wasu wuraren da suke ganin sun fi samun tsaro, sakamakon fargabar sake kai wani hari.
Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce zai mayar da martani bayan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sandan ta Katsina bai sake mayar da martani ba.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kakaba haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani manomi a ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue ya tsere daga muhallinsa sakamakon matsin lamba da barazana daga 'yan bindiga wadanda suka nemi ya biya su N500,000.
Manomin, wanda mazaunin gundumar Mbagena ne, ya shiga wannan halin ne sakamakon ƙaruwar ayyukan 'yan bindiga da suke karɓar haraji da kuɗin amfanin gona daga hannun mazauna yankin.
'Yan bindigan sun fara ba shi wa'adin kwana uku ne kawai, amma daga baya suka ƙara masa wa'adin zuwa mako guda bayan ya bayyana musu cewa ba shi da kuɗi a hannu har sai ya girbe amfanin gonarsa.
Asali: Legit.ng

