Abba Ya Yi Garambawul a Gwamnati, Ya Yi Sababbin Nade Nade a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sauye-sauyen masu ba shi shawara domin inganta aiki a gwamnatin jihar Kano
- An soke wasu mukaman masu ba da shawara tare da mayar da masu rike da su zuwa sababbin mukamai saboda wasu dalilai
- Gwamnan ya amince da nadin sababbin masu ba shi shawara, daga ciki har da tsohon Sakataren yaɗa labaran APC a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da yin wasu sauye-sauye a majalisar gwamnati ta hanyar sauya wa wasu masu ba shi shawara mukamai.
Haka kuma gwamnan ya amince da waɗansu sababbin nade-naden domin karfafa tsarin mulki da inganta ayyukan gwamnati.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, 2026 kuma ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
"Suna tare cikin daki"; Tsohon jami'in DSS ya fadi abin da ya kashe Janar Sani Abacha
Abba ya yi garambawul a Kano
A cewar sanarwar, an kuma soke ofisoshin mai ba gwamna shawara kan harkokin cikin gida na gidan gwamnati da kuma mai ba da shawara kan ofisoshin hulda da ke Abuja.
Daga bisani an mayar da wadanda ke rike da wadannan mukamai zuwa wasu sababbin wurare domin su ci gaba da aiki.
Sanarwar ta ce an mayar da Habiba Barwa, wadcce ta kasance mai ba gwamna shawara kan harkokin cikin gida na gidan gwamnati, zuwa mukamin mai ba da shawara kan ayyuka na musamman da suka shafi mata.
Haka kuma, Umar Akawu wanda ya kasance mai ba da shawara kan ofisoshin hulda da ke Abuja, ya koma mukamin mai ba da shawara a ofishin majalisar zartarwa mai kula da harkokin siyasa.
Ahmed Afuwa ta samu muƙami a Kano
Sauran wadanda sauye-sauyen suka shafa sun hada da Akibu Isa Murtala wanda aka mayar daga mai ba da shawara kan harkokin gudanarwa a ofishin gwamna zuwa mai ba da shawara kan kula da ma'aikata.
An kuma sauya wa Ibrahim Adam mukami daga mai ba da shawara kan yada labarai zuwa mai ba da shawara kan kafafen sada zumunta.
Nasiru Isa Dikko kuwa ya koma daga mai ba da shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu zuwa mai ba da shawara kan shirye-shiryen tallafa wa jama'a da bunkasa rayuwarsu.

Source: Facebook
A bangaren nade-nade, gwamnan ya amince da nada Bello Nuhu Bello a matsayin mai ba da shawara kan harkokin gudanarwa a ofishin gwamna. Kafin nadin nasa, yana matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin gudanarwa.
Haka zalika, tsohon sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a Kano, Ahmed Muhammad Aruwa, ya samu mukamin mai ba gwamna shawara kan harkokin yada labarai.
Sauran wadanda aka nada sun hada da Buhari Sule Kura a matsayin mai ba da shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu da Yahuza Ado Yankaba a matsayin mai ba da shawara kan tashoshin mota.
Sauran sababbin masu ba da shawara sun hada da Ahmed Tijjani Musa, Ibrahim Hamisu Rimi, Mustapha Abdullahi Rabiu Kura, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, Naziru Abdullahi Karaye da Tahir Ado Rabiu.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa an yi garambawul din ne domin kara inganta tafiyar da gwamnati, bunkasa hidimar jama'a da kuma tabbatar da cewa cibiyoyin gwamnati suna aiki daidai da manufofin gwamnati.
Abba ya yi nadi bayan komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da sababbin nade-nade da karin mukamai bayan sauya shekarsa zuwa APC.
Sanawar da Darekta janar kan yada, Sanusi Bature D-Tofa ya fitar ce ta tabbatar da karin nade-naden da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi don inganta Kano.
Ya kuma lissafa mutane bakwai da gwamnatin Kano ta daga likkafarsu, tare da bayyana dalilan da suka jawo aka yi sababbin nade-naden a wannan lokaci.
Asali: Legit.ng

