‘Yan Bindiga Sun Kashe Uba da Yaro sannan Sun Yi Garkuwa da Surukarsu a Sokoto
- 'Yan bindiga sun far ma wani gida a Sokoto, suka kashe ma'aurata da 'yan uwa tare da yin awon gaba da mata
- Wadannan miyagun ‘yan bindigan sun kai harin ne cikin dare, suka kashe mutane biyu nan take a kauyen
- Wannan lamari na garkuwa da mutane ya tsananta tsoro da fargabar 'yan bindiga a tsakanin mazauna yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sokoto - ‘Yan bindiga sun hallaka wasu mutane a wata barna da miyagun suka yi a karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.
‘Yan fashin daji sun kashe mutane biyu sannan sun yi garkuwa da wasu bayin Allah akalla 11 a hare-hare dabam-dabam da suka kai.

Source: Getty Images
Sokoto:'Yan bindiga sun fitini Goronyo
Wani rahoto na Daily Trust ya ce wadannan mummunan lamura a kauyukan Taloka da Hudu a karamar Goronyo da ke jihar Sokoto.
A cewar wani mazaunin Taloka, gomman ‘yan bindiga sun shigo kauyensu a kan babura 20 da kimanin karfe 12:30 na daren Laraba.
Mutumin yake cewa sun ji karan bindigogin lokacin da wadannan miyagu suka auko cikin kauyen suna bin jama’a gida zuwa gida.
Ya ce ‘yan bindigan sun fara shiga wani daki ne da matasa suka saba kwana a ciki.
Duk da matasan da ke kwance sun yi nasarar tserewa, amma abin takaicin shi ne ‘yan bindigan sun tafi da wani saurayi guda daya.
An dauke mutane a gidan wasu mutane
Ana haka sai ‘yan bindigan suka burma gidan wani mai suna Alhaji Yusuf, suka dauke shi tare da diyarsa da kuma wata surukarsa.
Abin bai tsaya a nan ba, sun bindige wani ‘dan ‘danuwan mutumin wanda aka bayyana sunan shi da Abdullahi Dan Almajiri inji rahoton.
A gidan wani Mallam Gado Dan Tsohuwa, 'yan ta'addan sun dauke wasu matan aure biyu, sannan suka shiga gidan Malam Alu Kansila.
Ko a gidan Kansila, sai da suka yi awon gaba da kananan yara biyu - mace da namiji.
Shi kuwa Alhaji Yusuf da aka fara tafiya sai ya fada wa ‘yan bindigan cewa sam ba zai iya cigaba ba saboda yanayin jikin shi.
A nan take suka harbe shi, suka bar gawar a nan, wanda mutane suka gani daga baya kuma aka yi mata sallah, aka birne ta.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun sace manoma a kauyen Sokoto
A kauyen Huda, an shiga gonaki an dauke wasu manoma da safiyar ranar Litinin. Za a samu labarin a jaridar nan ta Leadership.
Cikin wadanda aka dauke akwai Samaila Salisu, Musa Abdu, Naziru Saidu and Dan Abu Abdulkarim da kuma wain Basiru Bawa.
Daga baya an sako Malam Bawa, amma an ce wannan shi ne hari na 11 da aka kai wa kauyen, abin da ke nuna karfin matsalar tsaro.
Sokoto: 'Yan bindiga sun fatattaki bayin Allah
Kwanaki 'yan bindiga sun kai hare-hare a ƙauyuka sama da 30 a gundumar Danchadi da ke ƙaramar hukumar Bodinga a jihar Sokoto.
Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane shida, sace dabbobi sama da 1,000, da kuma raba daruruwan mazauna da muhallansu.
Rahoto ya ce Hakimin Danchadi ya mika rahoto ga hukumomi da jami'an tsaro domin neman dauki a gaggauta dawo da tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng


