Shugaba Tinubu Ya Maida Hankali kan Samar da Ayyuka Masu Gwabi ga Matasan Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Maida Hankali kan Samar da Ayyuka Masu Gwabi ga Matasan Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya maida hankali kan fadada damar samun ilimi da horo ga matasa yan Najeriya
  • Hadimin shugaban kasa kan harkokin dalibai, Kwamared Sunday Asfon ne ya bayyana hakan a bikin ranar matasa ta duniya
  • Ya bukaci matasa su rungumi sababbin dabaru, zaman lafiya da taimakon juna domin dogaro da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Dalibai, Kwamred Sunday Asefon, ya sake jaddada kudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sama wa matasa ayyukan yi.

Ya ce Shugaba Tinubu ya maida hankali wajen fadada damar samun ilimi, bunkasa kirkire-kirkire da samar da damarmakin aiki masu kyau ga matasan Najeriya.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a fadar gwamnatin tarayya Hoto: @aonanuga1956/X
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta rahoto cewa Asefon ya bayyana hakan ne ranar Laraba a sakonsa ga matasan Najeriya domin tunawa da ranar matasa ta duniya ta 2026.

Kara karanta wannan

Ana korafi a kan zargin lakadawa Musa Mai Sana'a duka kan tallan Tinubu a Katsina

Matasan Najeriya na da buri iri daya

Ya ce taken ranar matasa ta bana ya nuna irin burin da matasa ke da shi duk da bambancin yanayinsu da wuraren da suke rayuwa.

Ya ce daga cikin wadannan buri akwai samun ingantaccen ilimi, aikin yi mai kyau, kirkire-kirkire, hada kai, tsaro da kuma damar amfani da baiwa wajen samar da tasiri mai amfani ga al’umma.

A cewarsa, hulda da dalibai da matasa a jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi ta kara tabbatar masa da cewa bai kamata a rika kallon matasan Najeriya a matsayin shugabannin gobe kawai ba.

Ya ce ya kamata a dauke su a matsayin abokan hadin gwiwa wajen gina Najeriya ta yau da kuma makomar kasar.

Gwamnatin Tinubu na tallafa wa matasa

Asefon ya ce gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar samar da yanayin da zai bai wa matasan Najeriya damar samun kwarewar da ake bukata, samun ilimi, cin gajiyar damarmakin zamani da kuma bunkasa harkokin kasuwanci.

Kara karanta wannan

'Ina N4tr suka shiga"? Atiku ya kalubalanci Tinubu kan farfado da matatun mai

Ya ce gwamnati na aiwatar da shirye-shirye a fannonin ilimi, bunkasa kwarewa, amfani da fasahar zamani, tallafa wa dalibai, kasuwanci da kirkire-kirkire domin tabbatar da cewa babu wani matashi da aka bari a baya.

Ya ce:

“Bambancin yanayin da muke ciki bai kamata ya zama katanga ga burinmu na bai daya ba. Ko matashi yana Legas ko Lafia, Enugu ko Ekiti, Kano ko Calabar, burinmu yana hade da sha’awar ganin Najeriya ta zama kasa mafi kyau.”
Comrade Sunday Asefon
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin dalibai, Kwamared Sunday Asefon Hoto: @ayowole_obi
Source: Facebook

Ya bukaci matasa su tashi tsaye

Hadimin shugaban kasar ya bukaci matasan Najeriya da su daina kallon kansu a matsayin masu cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati kawai, su rungumi rawar da za su taka wajen samar da irin Najeriya da suke muradi.

Ya bukaci matasa su rungumi kirkire-kirkire, su koyi sabbin dabaru, su inganta zaman lafiya, su yi watsi da tashin hankali tare da taimakon juna.

Abubakar Sulaiman, wani matashi a Katsina ya ce akwai abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi matukar tana son sama wa matasa ayyukan yi.

Da yake hira da wakilinmu, matashin wanda aka fi sani da Habu ya ce wutar lantarki na daya daga cikin muhimmn abubuwan da ke rage zaman kashe wando tsakanin matasa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji yadda ta kaya tsakanin wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC

"A ganina shirye shiryen da gwamnati ke kirkirowa da bayar da horo suna da amfani amma akwai abubuwan da ya kamata a gyara idan ana son matasa su nemi na kansu.
"Wutar lantarki na taka muhimmiyar rawa sabida akwai sana'o'in da ke bukatar wuta amma babu, dole sai dai ka sayi inji ga tsadar fetur. Ni ina ganin tallafin da ake rabawa da wasu horarwa da akw shirya wa ba su ne mafita ba," in ji shi.

Gwamnati za ta samar da ayyuka 50,000

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da Tinubu Light Initiative (TLI ) , wani shiri na samar da makamashin lantarki mai tsafta a faɗin ƙasa.

na sa ran wannan shiri zai samar da ayyukan yi kai tsayelsama da 50,000, ga matsa yan Najeriya tare da rage farashin gudanar da kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262