Bidiyo Ya Fara Yawo, An Fallasa Yadda Kwankwasso Ya Karkatar da Biliyoyin Naira a Kano

Bidiyo Ya Fara Yawo, An Fallasa Yadda Kwankwasso Ya Karkatar da Biliyoyin Naira a Kano

  • Tsohon shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya budo shafin Rabiu Kwankwaso
  • Muhyi Magaji ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya karbi biliyoyin Naira daga baitul malin jihar Kano domin gudanar da harkokinsa
  • Kungiyar Kwankwasiyya ta ce tana nazarin zarge-zargen da tsohon shugaban hukumar PCACC ya yi kuma za ta mayar da martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano, Nigeria - Tsohon Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barrista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya tono badakalar Sanata Rabiu Kwankwaso.

Muhyi ya zargi dan takarar mataimakin shugaban kas na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da karkatar da biliyoyin Naira daga kudaden jihar domin amfanin kansa.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Kano Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa Muhyi Magaji ya kalubalanci Kwankwaso da ya garzaya kotu idan har zarge-zargen da yake yi ba gaskiya ba ne.

“Ina kalubalantar ka da ka kai ni kotu idan abin da na ce ka fitar daga baitul malin Kano ba gaskiya ba ne,” in ji Muhyi.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci za a rataye jagoran dabar yan bindiga Jibrin Halilu har lahira

Muhyi Magaji ya dura kan Kwankwaso

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta kuma daga baya ya tabbatar da sahihancinsa, Muhyi ya yi zargin cewa Kwankwaso ya karbi makudan kudi daga asusun gwamnatin Kano ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.

A cewarsa, an bai wa Kwankwaso Naira biliyan daya a watan Disamban 2023 domin gina gidansa, amma bai bayyana ko gidan da ake magana a kai shi ne wanda tsohon gwamnan ke zaune a ciki ba.

Muhyi ya kuma yi ikirarin cewa an ba Kwankwaso Naira miliyan 525 domin gina ofishi, sannan ya karbi Naira biliyan 1.240 da kuma karin Naira miliyan 400 domin sayen motoci.

Haka zalika, ya ce a watan Yunin 2024, Kwankwaso ya karbi Naira miliyan 100.8 domin kula da lafiyarsa, ya kuma karbi Naira miliyan 510.213 a matsayin kudaden hutu.

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hancin ya ce akwai karin bayanai da yake da su kan yadda aka yi amfani da kudaden jama’a ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Mutuwar Janar Rabe: Kwankwaso ya kai ziyara Katsina, ya bada mafita kan matsalar tsaro

Muhuyi Magaji.
Tsohon shugaban hukumar PCACC, Barista Muhyi Magaji Rimin-Gado Hoto: Amb Hafizu Aminu Daiba
Source: Facebook

Kwankwasiyya ta maida martani

Da aka tuntubi mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Muhammad Sale Mailemo, ya tabbatar da cewa sun samu labarin zarge-zargen.

Ya ce:

“Muna nazarin zarge-zargen kuma za mu mayar da martani yadda ya dace, ciki har da yiwuwar daukar matakin shari’a kan Barrista Muhyi.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rabiu Musa Kwankwaso bai fito ya mayar da martani kai tsaye kan zarge-zargen ba.

Haka kuma, Muhyi bai gabatar da wata hujja a bainar jama’a da ke tabbatar da ikirarinsa ba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Bugu da kari, babu wata kotu ko hukuma mai yaki da cin hanci da ta sanar da samun wata hujja ko sakamakon bincike da ke danganta Kwankwaso da wadannan zarge-zarge.

Kwankwaso ya soki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa 'dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya soki gwamnatin Najeriya kan rashin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya gana da jagororin tafiyar Obi da Kwankwaso

Kwankwaso ya ce fashi da makami, garkuwa da mutane, ta’addanci, rikice-rikice da kuma fashin makami sun zama ruwan dare a kasar nan.

Ya yi kira da a ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, da ƙara tattara bayanan sirri, da bunƙasa aikin ’yan sandan al’umma, tare da ɗaukar matakan magance tushen matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262